Mutane 24 Sun Mutu a Wani Hatsarin Jirgin Ruwa a Jihar Neja

Mutane 24 Sun Mutu a Wani Hatsarin Jirgin Ruwa a Jihar Neja

  • Wani jirgin ruwa ɗauke da manoma masu yawa ya gamu da hatsari a yankin Mokwa na jihar Neja
  • Jirgin ruwan ya ɗauko manoman ne daga ƙauyen Gbajibo zuwa Tungan-Mangu inda ya gamu da hatsari a kan hanyarsa
  • Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin amma ba su bayyana adadin yawan mutanen da hatsarin ya ritsa da su ba, da kuma waɗanda suka rasa ransu

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Neja - Wani iftila'i ya auku a jihar Neja da safiyar ranar Lahadi, 10 ga watan Satumba, bayan wani jirgin ruwa ya yi hatsari a yankin Mokwa na jihar.

Ba a san adadin yawan mutanen da ke cikin jirgin ruwan ba, sannan ba a san takamaiman abin da ya haddasa haɗarin ba har ya zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Mutane da dama sun rasu a wani hadarin jirgin ruwa a Neja
Jirgin ruwan yana dauke ne da manoma Hoto: Vanguard.com
Asali: UGC

Da yake magana da Channels tv ta wayar tarho, shugaban ƙaramar hukumar Mokwa, Jibrin Abdullahi Muregi, ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewa ana cigaba da ƙoƙarin ceto mutanen da hatsarin ya ritsa da su.

Kara karanta wannan

Kaico: Yadda Yan Bindiga Suka Halaka Matar Aure a Gaban Idon Mijinta

Ya tabbatar da cewa an ciro gawarwakin mutum 21, inda ya ƙara da cewa mutanen da hatsarin ya ritsa da su sun fito ne daga ƙauyukan Gbajibo, Ekwa da Yankeiade na ƙaramar hukumar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar hatsarin

Jaridar Daily Trust ta ce jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa sun bayyana cewa suna karɓar bayanai domin tantance adadin mutanen da ke cikin jirgin, amma sun tabbatar da aukuwar hatsarin.

Lokacin da aka tuntuɓi kakakin rundunar ƴan sandan jihar, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da aukuwar hatsarin.

Sai dai, ya bayyana cewa bayanan da ƴan sanda suka samu sun nuna cewa mutum 13 ne suka rasa rayukansu a hatsarin

"Bayanan da muka samu daga yankin Gbajibo na ƙaramar hukumar Mokwa ya nuna cewa wani jirgin kwale-kwale mai ɗauke da fasinjoji daga Gbajibo zuwa Tungan-Mango domin aikin gona ya kife." A cewarsa.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Hatsarin Jirgin Ya Laƙume Rayukan Mutane Sama da 10 a Jihar Arewa

Mutum 15 Sun Rasu a Hatsarin Jirgin Ruwa

A wani labarin na daban kuma, kun ji cewa aƙalla mutane 15 suka mutu yayin da wani jirgin ruwa da ya ɗauko Fasinjoji harda kananan yara ya yi hatsari a jihar Adamawa.

Hatsarin ya faru ne lokacin da Jigin Kwale-Kwalen, wanda ya ɗauko ƴan kasuwa, kananan yara da manoma ya taso daga ƙauyen zuwa Yola.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng