Al’ummar Yarbawa Sun Yi Wa Kwankwaso Da Gwamnatin Kano Addu’a Ta Musamman

Al’ummar Yarbawa Sun Yi Wa Kwankwaso Da Gwamnatin Kano Addu’a Ta Musamman

  • An gudanar da taron addu'a ta musamman ga gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnati mai ci don nema masu kariyar Allah
  • Al'ummar Yarbawa mazauna jihar Kano ne suka yi wannan taro a ranar Asabar, 9 ga watan Satumba
  • Sun nemi Allah ya kare jagoran Kwankwasiya daga sharrin makirai masu yi masa zagon kasa a cikin jam'iyyar NNPP

Al'ummar Yarbawa mazauna Kano sun gudanar da taron addu'a ta musamman don neman Allah ya yi wa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da gwamnati mai ci jagoranci da kare su.

Taron addu'an wanda aka gudanar a ranar Asabar, 9 ga watan Satumba a yankin Sabongari da ke jihar, ya samu halartan mabiya addinin Musulci da kiristanci.

Al'ummar Yarbawa sun yi taron addu'a ta musamman a Knao
Al’ummar Yarbawa Sun Yi Wa Kwankwaso Da Gwamnatin Kano Addu’a Ta Musamman Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Ba a taba shugaban da talakawa suka ji dadinsa irin Kwankwaso ba, Yarbawan Kano

Kara karanta wannan

Jam'iyyar PDP Ta Zargi Gwamnan Jihar Arewa Da Lalata N20bn A Iska, Ta Tona Asirin Yadda Aka Yi Da KudIN

Al'ummar sun hadu sun roki Allah ya hana makirai da ke yi wa Kwankwaso zagon kasa a jam'iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) cin galaba a kansa, rahoton Daily Trust.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wanda ya shirya taron, Abdulsalam Abiola Abdullateef ya jaddada cewar sun yanke shawarar haduwa don yin addu'o'in ne saboda sun fahimci muhimmancin zaman lafiya wajen samun ci gaba.

Ya ce sun yi addu’ar ne don neman taimakon Allah kan kalubalen da babban jagoran jam’iyyar NNPP na kasa ke fusakanta a halin yanzu da kuma nasarar gwamnatin Kano ta kotun zabe.

Abdullateef ya bayyana cewa babu wani shugaban Najeriya da ya zuba jari a karatun talakawa da walwalar al’umma kamar Kwankwaso, rahoton Independent.

Abdullateef ya ce:

"Mun roki Allah madaukakin sarki da ya kare Gwamna Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa, Kwamrad Aminu Abdussalam da nagartacciyar gwamnatin da suka sanya a gaba, mutanen Jihar Kano masu mutunci, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso da kansa da kuma jam’iyyar NNPP."

Kara karanta wannan

"Ku Taimaka Mana" Ministan Tinubu Ya Roƙi Yan Najeriya Alfarma 1 Tak, Ya Ce Akwai Matsala

Gwamnatin Kano ta saki kudi biliyan 4.8 don gudanar da ayyuka daban-daban

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin jihar Kano ta ce ta amince da sakin kudi naira biliyan 4.8 domin aiwatar da ayyuka daban-daban a jihar.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X da aka fi sani da Twitter a ranar Asabar, 9 ga watan Satumba.

Ya ce majalisar zartarwa ta jihar yayin zamanta na ranar Alhamis da ta gabata, ta amince da sakin kudi kimanin N79,284,538 domin fara aikin gyaran makarantun sakandare na kwana guda 11.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel