Kotun Zabe Ta Sake Tsige Wani Dan Majalisar Tarayya Na LP, Ta Maye Gurbinsa Da Wani

Kotun Zabe Ta Sake Tsige Wani Dan Majalisar Tarayya Na LP, Ta Maye Gurbinsa Da Wani

  • Kotun zabe da ke zama a Enugu ta tsige Chijioke Okereke na jam'iyyar Labour Party (LP) a matsayin dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Aninri/Awgu/Oji River
  • Okereke shine dan jam'iyyar LP na biyu da kotun zaben ke tsigewa bayan an maye gurbin Farfesa Paul Sunday Nnamchi da Cornelius Nnaji, dan takarar PDP
  • Zargin da ake yi wa Okereke shi ne cewa INEC ba ta buga sunansa a matsayin dan takarar jam’iyyar LP ba kuma sunan sa ba ya cikin takardar sakamakon

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Enugu - Kotun sauraron kararrakin zabe yan majalisun tarayya da ke zama a Enugu ta tsige Chijioke Okereke na jam'iyyar Labour Party (LP).

Har zuwa lokacin da aka tsige shi a ranar Juma'a, 8 ga watan Satumba, Okereke ne dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Aninri/Awgu/Oji-River.

Kara karanta wannan

Duka Sanatoci da ‘Yan Majalisun Tarayya 9 da Aka Tsige a Kotun Sauraron Karar Zabe

Dan majalisar tarayya na LP ya sha kaye a kotun zabe
Kotun Zabe Ta Sake Tsige Wani Dan Majalisar Tarayya Na LP, Ta Maye Gurbinsa Da Wani Hoto: @csoproject
Asali: Twitter

Kotun zaben Enugu ta ayyana dan takarar PDP a matsayin wanda ya lashe zabe

Da hukuncin kotun zaben, Okereke ya zama dan majalisar tarayya na LP na biyu da kotun zaben ta tsige cikin awanni 24, jaridar Guardian ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ku tuna cewa a ranar Juma'a ne kotun sauraron korafe-korafen zaben majalisar dokoki da ke zama a Enugu ta soke zaben dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Enugu ta gabas/Isi-Uzo, Farfesa Paul Nnamchi. Nnamchi, jigon LP.

Kan Okereke, alkalan kotun zaben karkashin jagorancin Mai shari'a Nusirat Umar ta ayyana Anayo Onbwuegbu, dan takarar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a matsayin zababben dan takara a zaben na ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

Onwuegbu ya tunkari kotun zaben inda yake kalubalantar ayyana Okereke a matsayin wanda ya lashe zaben kan cewa shi bako ne a zaben domin babu sunansa a sakamakon a matsayin dan takarar LP.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kotun Zabe Ta Tsige Dan Majalisar Tarayya Na PDP a Bayelsa, Ta Soke Zaben

Kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto, kwamitin kotun ya riki cewa Okereke ba shine dan takarar zaben ba sannan ya umurci hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta (INEC) da ta bai wa dan takarar na PDP takardar shaidar cin zabe.

Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Dan Majalisar APC a Jihar Benue

A wani labarin, kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisar jihar Benue mai zamanta a birnin Makurdi, a ranar Asabar ta tabbatar da nasarar Philip Agbese, na jam'iyyar APC a kujerar ɗan majalisan Ado/Okpokwu/Ogbadibo.

Abokan takararsa na jam'iyyun Peoples Democratic Party da Labour Party, Aida Narth da Ralph Ogbodo, sun maka Agbese a kotu bayan nasarar da ya samu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, cewar rahoton Daily Trust.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng