Manyan Labarai A Yau
Gamayyyar ƙungiyoyin magoya bayan jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na ƙasa, sun buƙaci shugaban ƙasa Tinubu ya maye gurbin ministan Kaduna da shugabansu.
Rikicin filaye da iyakoki a tsakanin wasu ƙauyuka huɗu na ƙaramar hukumar Yala a jihar Cross Rivers, ya sanya gwamna Bassey Otu sanya dokar hana fita.
Magoya bayan Tajudeen Baruwa da Badru Agbede sun sanya mutanen Abuja cikin firgici bayan sun ɓarke da rikici wanda har harbe-haben bindigu aka yi.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen ƴan majalisun tarayya a jihar Kano, ta zartar da hukuncinta kan ƙarar da Kabiru Gaya na APC ya shigar da Kawu Sumaila na NNPP.
Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Fasto Elijah Babatunde Ayodele ya hango gwamnoni huɗu da kotu ba za ta ƙwace nasarar da suka samu a zaɓe ba.
Tsohon gwamnan jihar Legas, Babatunde Raji Fashola ya bayyana cewa zai taka rawarsa a matsayinsa na ɗan ƙasa a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓe mai zamanta a birnin Jos, babban birnin jihar Pƙateau ta soke zaɓen ɗan majalisar PDP, Dachung Musa Bagos, ta ba ɗan LP nasara.
Wani ɗan Najeriya da ya yi hijira zuwa ƙasar Canada domin samun ingantacciyar rayuwa, ya tattaro ƴan komatsansa ya dawo gida Najeriya saboda rashin aikin yi.
Tsohuwar shugabar hukumar NDDC, Lauretta Onochie na son hukumar ƴan sandan farin kaya ta cafke Peter Obi na jam'iyyar Labour Party kan zargin iza wutar rikici.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari