Yan Bindiga Sun Kashe Fastoci 23 Tare Da Rufe Cocina Sama Da 200 a Kaduna, Kungiyar CAN Ta Koka

Yan Bindiga Sun Kashe Fastoci 23 Tare Da Rufe Cocina Sama Da 200 a Kaduna, Kungiyar CAN Ta Koka

  • An rahoto cewa yan ta'adda sun kashe fastoci 23 sannan an rufe cocina sama da 200 a jihar Kaduna cikin shekaru hudu da suka gabata
  • Shugaban kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) a jihar Kaduna, Rev. John Hayab, ne ya bayyana haka a ranar Talata, 12 ga watan Satumba
  • Da yake jawabi a wani taron gaggawa, Rev. Hayab ya ce fastoci da dama sun gaza ci gaba saboda an kona cocinansu

Jihar Kaduna - Kungiyar kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna, ta ce yan bindiga sun kasge akalla fastoci 23 kuma an rufe cocina guda 200.

Kamar yadda SaharaReporters ta rahoto, shugaban kungiyar CAN a Kaduna, Rev. John Hayab, ne ya bayyana haka a wani taron gaggawa tare da kwamishinan yan sanda na jihar, Musa Garba da fastocin jihar a ranar Talata, 12 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

EFCC ta Cafke Mutumin Jonathan da Orubebe, An Yanke Masu Daurin Shekaru 6

Kungiyar CAN ta koka kan barnar da yan bindiga suka yi masu a jihar Kaduna
Yan Bindiga Sun Kashe Fastoci 23 Tare Da Rufe Cocina Sama Da 200 a Kaduna, Kungiyar CAN Ta Koka Hoto: Nigeria Police Force
Asali: Facebook

Yan bindiga sun kashe fastoci 23, sun rufe cocina 200

"Mun rasa fastoci 23 a hannun yan bindiga a Kaduna cikin yan shekaru da suka gabata. Na baya-bayan nan shine kisan fasto Rabaran Jeremiah Wayo lokacin da ya je gonarsa a Kujama da ke karamar hukumar Chikun."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, Rev. Hayab ya kara da cewar fastoci da dama sun gaza ci gaba saboda an kona cocinansu.

"Bari na fada maka annan, kwamishina, cewa yan bindiga sun rufe sama da cocina 200. Cocin Baptist na da sama da cocina 100 da aka rufe. Daga Birnin Gwari zuwa Chikun da Kajuru, cocinan basa nan kuma."

A martaninsa, CP Garba ya ce bai kamata a dunga daukar miyagu a matsayin Kirista ko Musulmi ko kabilu da al'adunsu ba.

"Abun takaici ne cewa shugaban CAN ya ambaci kimanin malamai 23 da yan bindiga suka kashe a jihar Kaduna a lokuta daban daban. Abun takaici ne.

Kara karanta wannan

Wike Ya Yi Babban Albishir Ga Yan Najeriya Kan Gwamnatin Tinubu, Ya Ce Romon Dadi Na Nan Tafe

"Sai dai kuma, wadannan abubuwan ba wai ga malaman kirista kawai yake faruwa ba, ya faru ga kusan kowa saboda masu laifi basu da kabila, basu da addini. Miyagu basu da tausayi, miyagu mugwaye ne."

Kungiyar CAN ta nemi mazauna Kaduna su kare kansu daga hare-haren 'yan bindiga

A wani labarin, mun ji a baya cewa kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) reshen jihar Kaduna, ta yi kira ga mazauna kudancin Kaduna da ma sauran garuruwan da ke jihar baki daya da su tashi tsaye wajen kare kawunansu daga hare-haren 'yan ta'adda.

Shugaban kungiyar CAN na jihar Kaduna, John Joseph Hayab ne ya bayyana hakan yayin da yake martani kan harin da 'yan bindigan suka kai a wata coci da ke Kafanchan, ƙaramar hukumar Zangon Kataf.

Asali: Legit.ng

Online view pixel