Lauretta Onochie Na Son DSS Ta Yi Carar Da Peter Obi, Ta Fadi Dalilanta

Lauretta Onochie Na Son DSS Ta Yi Carar Da Peter Obi, Ta Fadi Dalilanta

  • An shigar da koke ga hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) da ƴan sanda su cafke Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party
  • Lauretta Onochie tsohuwar shugabar hukumar NDDC ita ce ta shigar da wannan ƙorafin a soshiyal midiya a ranar ranar Talata, 12 ga watan Satumba
  • Ta zargi Peter Obi da iza wutar rikici sannan ta bayyana shi a matsayin wawa wanda yake son mulki ko ta halin ƙaƙa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Tsohuwar shugabar hukumar NDDC, Lauretta Onochie, ta yi bayanin dalilin da yakamata a ce ƴan sanda da hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) sun cafke Peter Obi.

A wani dogon rubutu da ta yi a soshiyal midiya a ranar Talata, 12 ga watan Satumba, Onochie ta bayyana Peter Obi a matsayin wawa wanda yakamata ace an yi cafke shi.

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Bayyana Abin Da Atiku, Peter Obi Za Su Tarar a Kotun Koli

Lauretta Onochie ta bukaci DSS su cafke Peter Obi
Lauretta Onochie na son DSS su kama Peter Obi Hoto: Mr Peter Obi/DSS/Lauretta Onochie
Asali: Facebook

Ta yi zargin cewa ƴan barandan Peter Obi su ne ke iza wutar rikici bayan rashin nasarar da ya yi a zaɓen shugaban ƙasa da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa.

Onochie ta rubuta:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sanin cewa baya da wata madafa, ya bari ƴan wanki sun yi masa wayau zuwa kotu kan abubuwan da tun da daɗewa kotun ƙoli ta gama hukunci a kansu."

Zarge-zargen Onochie akan Peter Obi

Ta zargi Peter Obi da jam'iyyar Labour Party wajen haɗa baki da ƙungiyar ƙwadago domin yin amfani da yajin aikin gargaɗi wajen kawo ruɗani a ranar da kotun sauraron ƙararrakin zaɓen shugaban ƙasa za ta zartar da hukuncinta.

Onochie ta rubuta:

"Lauretta Onochie ta yi kira ga DSS su gaggauta cafke Peter Obi na jam'iyyar Labour Party bisa zargin iza wutar rikici a Najeriya."

Kara karanta wannan

Babban Malamin Addini Ya Yi Hasashen Abin Da Zai Faru Ga Atiku, Peter Obi a Kotun Koli

"Wannan mutumin @PeterObi, yana cigaba da ingiza mabiyansa waɗanda ba su da ƙwaƙwalwa kan sauya gwamnati ta ƙarfin tsiya. Ɓan taɓa ganin wanda ya matsu irinsa ba.
"Akwai wani mugun abu da ban tsoro game da mutumin da ya zo na uku a zaɓen, kuma yana son a bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara, ta kowane hali!"
"Ina tunanin lokaci ya yi da yakamata a cafke shi domin ya amsa ƴan tambayoyi. Ƴan Najeriya na son sanin meyasa Peter Obi ya ƙosa irin haka."

Tinubu Na Shirin Daina Amfani Da Naira

A wani labarin kuma, an gudanar da bincike kan wani bidiyo wanda ya nuna Shugaba Tinubu na bayyana shirinsa na daina amfani da naira a koma dala a ƙasar nan.

Binciken da aƙa gudanar ya nuna cewa bidiyon sauuya shi aka yi, domin ba ainihin abinda shugaban ƙasan ya bayyana ba ne a cikin bidiyon.

Asali: Legit.ng

Online view pixel