Dan Najeriya Ya Tattaro Ya Dawo Gida Daga Kasar Canada Saboda Rashin Aikin Yi

Dan Najeriya Ya Tattaro Ya Dawo Gida Daga Kasar Canada Saboda Rashin Aikin Yi

  • Wani mutumi ya koma ƙasar Canada domin samun rayuwa mai kyau amma ya dawo Najeriya bayan abubuwa sun kwaɓe masa
  • Mutumin mai suna @iaboyeji, ya bayyana cewa ya shiga damuwa da rashin aikin yi a Canada, kawai sai ya yanke shawarar ya dawo gida
  • Aboyeji, wanda ɗan kasuwar fasaha ne, ya bayyana lokacin bizar karatunsa ya kusa ƙarewa kuma abubuwa ba su gyaru masa ba kamar yadda ya so

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Wani mutumi ya bayyana yadda ya tattaro ƴan komatsansa ya dawo Najeriya bayan ya fuskanci ƙalubale a ƙasar Canada.

Mutumi mai suna @aiaboyeji, ya bayyana cewa tafiyarsa zuwa Canada domin samun rayuwa mai kyau ba ta haifar da ɗa mai ido ba.

Dan Najeriya ya dawo gida daga Canada
Ayodeji ya ce ya shiga damuwa sosai saboda rashin aikin yi a Canada Hoto: @iaboyeji/Getty Images/Aaron Foster.
Asali: UGC

Bayan ya koma Canada, Aboyeji ya bayyana cewa dole ya dawo gida saboda damuwa da ta yi masa yawa.

Kara karanta wannan

Rayuwa Juyi-Juyi: Na Taba Yin Gadi, Ilmi Ya Jawo Na Zama Shugaban Kasa - Tinubu

Dalilin da yasa ɗan Najeriya ya dawo bayan ya koma Canada

A wani rubutu da ya yi a Twitter, ya bayyana lokacin da ya sanya a bizarsa zai yi a Canada na ta ƙara matsowa, kuma har yanzu ya kasa samun abin da yake so.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rashin samun aikin yi da ya yi ya ƙara dagula masa lissafi inda ya koma zaman kashe wando.

Hakan ya sanya damuwa ta yi masa yawa, inda a daidai wannan lokacin ne ya fahimci cewa gida Najeriya kawai zai dawo.

Yana yin martani ne akan wani rubutu da aka yi a Twitter inda aka tambayi mutane su bayyana dalilin da ya sanya suka dawo Najeriya bayan sun koma ƙasar waje.

A kalamansa:

"Na shiga damuwa sosai a Canada. Ba kuɗi, ba aiki. Lokacin bizar karatuna ya kusa ƙarewa kuma ɗan kamfanin da na fara ginawa bai yi nasara ba. Na yi tunanin cewa idan har ina yin haka a Canada, Najeriya ba za ta fi taɓarɓarewa haka ba, don haka sai na dawo."

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Hatsarin Jirgin Ya Laƙume Rayukan Mutane Sama da 10 a Jihar Arewa

Ƴan soshiyal midiya sun yi martani

@tequaneV ya rubuta:

"Shin kamfanin ka ya yi nasara bayan ka dawo Najeriya ko wani aiki ka nema?"

@DebolaAlaka_ ya rubuta:

"Kasancewar mutane da yawa na mamaki mutane na dawowa Naija ya bayyana tunanin masu japa.. Jama'ar mu suna buƙatar canjin tunani sosai, sake wayar da kai."

@m_nda_yakubu ya rubuta:

"Wannan gaskiya ne! Sau da yawa a cikin ƙalubale da ƙunci ne muke gane ko su wanene mu da abin da ya fi muhimmanci a gare mu."

Magidanci Ya Tarar Da Kato a Dakinsa

A wani labarin kuma, wani magidanci ya cika da mamaki bayan ya dawo gida ya yarar da garjejen ƙato kwance akan gadonsa da matarsa.

Magidancin ya fusata inda ya kama ƙaton da faɗa domin jin ba'asi kan dalilin da ya sanya ya shigo masa gida ba tare da izninsa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel