Manyan Labarai A Yau
A ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba, kamfanin BUA yasanar da karya farashin buhun siminti zuwa N3,500. Za a fara sayar da kaya kan sabon farashin daga ranar Litinin.
Wani mummunan hatsarin mota ya ritsa da mutane da dama akan titin hanyar Legas zuwa Ibadan. Mutum ɗaya ya rasa ransa yayin da wasu da dama suka raunata.
Gwamnatin tarayya a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoban 2023, ta sanar da ƙarin albashi da rabon tallafin kuɗi bayan ta kammala ganawa da ƙungiyar NLC.
Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi wa Shugaba Tinubu shaguɓe kan kan takardun bayanan karatunsa na jami'ar CSU.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce zanga-zangar ma’aikata kan tsige shugabannin hukumomi a Abuja baya damunsa domin dai abun da yake aikatawa shine daidai.
Shugaban kasa Tinubu ya amince da Karin albashin wucin gadi na N35,000 ga ma’aikata a dukkan mataki. Shugaban ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila ne ya sanar da hakan.
Shugabannin kungiyar kwadago na cikin ganawa mai muhimmanci da tawagar gwamnatin tarayya a fadar shugaban kasa gabannin shirin shiga yajin aikin gama gari.
Kungiyar kwadago ta yi kira al'ummar Najeriya da su shiga cikin tattakin neman yanci, inda ta dage cewa za ta shiga yajin aikin sai baba ta gani daga ranar Talata.
Yan Najeriya sun nuna rashin jin dadinsu kan hauhawan farashin gas din girki wanda ya kai N1,000 kan kowace kg bayan yan kasuwar fetur da gas sun yi gargadi.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari