Kamfanin Simintin BUA Ya Karya Farashin Siminti Zuwa N3,500 Kan Kowani Buhu

Kamfanin Simintin BUA Ya Karya Farashin Siminti Zuwa N3,500 Kan Kowani Buhu

  • Kamfanin BUA ya sanar da rage farashin buhun siminti domin saukaka wa al'ummar Najeriya samun damar yin gine-gine
  • Daga ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba, buhun simintin BUA zai koma kan farashin N3,500
  • Kamfanin ya kuma ce akwai yiwuwar ya sake rage farashin da zarar an kammala aikin sabbin layukan da yake zuwa 2024

Kamfanin simintin BUA, wanda shine kamfanin siminti mafi girma na biyu a kasuwar Najeriya, ya sanar da rage farashin buhun siminti zuwa N3,500.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X a ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoba, kamfanin ya ce sabon farashin zai fara tasiri daga ranar Litinin, 2 ga watan Oktoba.

Farashin buhun siminti a yanzu haka kafin fitar da sanarwar ya kai kimanin N5,000 kowani buhu daya.

Kara karanta wannan

Za a Fasa Shiga Yajin-Aiki a Najeriya, Gwamnati Ta Shawo Kan Kungiyoyin Ma’aikata

Kamfanin BUA ya karya farashin siminti
Kamfanin Simintin BUA Ya Karya Farashin Siminti Zuwa N3500 Kan Kowani Buhu Hot: Ba Cement
Asali: Facebook

Kamfanin BUA wanda yake mallakin attajirin dan kasuwa AbdulSamad Rabiu, ne yana da kayan aiki da ke iya samar da siminti tan miliyan 11.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin rage farashin simintin BUA

A cewar kamfanin, wannan wani mataki ne na saukaka wa al'ummar Najeriya samun damar yin gine-gine da kuma saukaka farashin kayan gini.

Har ila yau, kamfanin ya ce da zarar an kammala aikin sabbin layukan da kamfanin ke yi a halin yanzu, zuwa sabuwar shekara, akwai yiwuwar ya sake rage farashin.

Sanarwa ta ce:

"Dangane da bayanin da muka fitar a baya kan aniyarmu na rage farashin siminti da zarar mun kammala bude sabbin layukanmu a karshen shekara, domin bunkasa kayan gini da sashin gine-gine.
“A kokarinmu na rage farashin kayayyakinmu da sake nazari kan ayyukanmu lokaci zuwa lokaci, hukumar gudanarwa ta kamfanin BUA tana sanar da abokan kasuwancinta da masu ruwa da tsaki hadi da al’umma cewa daga ranar 2 ga watan Oktoban 2023, mun cimma matsayar rage farashin. Dangane da hakan, daga yanzu za a sayar da buhun simintin BUA a kan kudi naira 3,500 domin yan Najeriya su fara cin gajiyar farashin kafin mu kammala tsare-tsarenmu.”

Kara karanta wannan

"Tattakin Neman Yanci": Kungiyar Kwadago Ta Ce Babu Ja Da Baya a Yajin Aikin Da Take Shirin Zuwa

Za mu zuba ido kan yadda dillalai ke siyarwa jama'a kaya, BUA

Kamfanin ya kuma sanar da cewar duk wadanda suka riga suka biya kudin kaya a tsohon farashi da ba a kai masu ba za su ci gajiyar wannan ragi da aka yi daga ranar 2 ga watan Oktoban 2023.

Ya kuma yi kira ga dillalai masu lasisi da su tabbatar da ganin cewa masu siyan kaya a hannunsu sun ci gajiyar wannan raji da kamfanin ya yi inda ya sha alwashin sanya idanu don tabbatar da ganin an bi tsari wajen siyar da simintin.

Ga sanarwar a kasa:

Shugaba Tinubu ya gana da shugaban kamfanIn Bua, za a karya farashin siminti

A baya mun ji cewa shugaban rukunin kamfanonin BUA, Abdul-Samad Rabiu, ya ce kamfaninsa na ƙoƙarin rage farashin siminti a faɗin Najeriya.

Ya bayyana haka ne ranar Jumu'a, 15 ga watan Satumba yayin hira da manema labarai na fadar shugaban kasa jim kaɗan bayan ganawa da Bola Ahmed Tinubu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel