Yajin Aikin ASUU: Tinubu Ya Bada Umurnin a Biya Lakcarori Albashinsu Da Aka Rike

Yajin Aikin ASUU: Tinubu Ya Bada Umurnin a Biya Lakcarori Albashinsu Da Aka Rike

  • Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da soke tsarin "ba aiki, ba biya" da aka kakabawa mambobin kungiyar ASUU
  • Domin nuna jin kai ga malaman jami'a, Tinubu ya amince a biya su albashinsu na watanni hudu da aka rike
  • An rike albashin mambobin kungiyar ASUU na watanni takwas bayan shafe tsawon watanni suna yajin aiki a 2022

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince a biya albashin watanni hudu da aka rikewa malaman jami’o’i karkashin kungiyar ASUU.

Hakan ya biyo bayan jingine tsarin "ba aiki, ba biya" da aka kakabawa malaman ASUU kan shafe tsawon watanni takwas suna yajin aiki a 2022, jaridar The Nation ta rahoto.

Shugaban kasa Tinubu ya amince da biyan malaman ASUU albashin watanni 4 da aka rike masu
Yajin Aikin ASUU: Tinubu Ya Bada Umurnin a Biya Lakcarori Albashinsu Da Aka Rike Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin labarai, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba.

Kara karanta wannan

Wike: Tashin Hankali Yayin da Tsohon Kakakin APC Ya Bukaci Tinubu Da Ya Kama Sheikh Gumi

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, Ngelale ya ce an bayar da umurnin ne domin nuna jin kai ga malaman da kuma ganin lakcarorin sun samu albashin watanni hudu cikin watanni takwas din.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani bangare na sanarwar ya ce:

“A kokarinsa na rage matsalolin da ake fuskanta a lokacin aiwatar da muhimman sauye-sauyen tattalin arziki a kasar nan, tare da amincewa da aiwatar da tsare-tsaren da aka cimma a tattaunawar da aka yi tsakanin ASUU da gwamnatin tarayyar Najeriya, Shugaban kasa Bola Tinubu ya bayar da umarnin jingine batun “ba aiki, ba biya” da aka kakabawa ASUU, wanda zai bai wa mambobin Kungiyar ASUU damar karbar albashin watanni hudu (4) daga cikin na albashin watanni takwas da aka rike masu yayin yajin aikin watanni takwas da kungiyar ta tafi.”

Legit Hausa ta tuntubi wata malamar jami’a wacce ke cikin kungiyar ASUU don jin yadda ta samu wannan labari na biyansu bashin albashinsu.

Kara karanta wannan

Mista Ibu: Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki Ya Dauki Nauyin Asibitin Jarumin Da Ke Jinya

Malama Fati Abubakar ta ce:

“Na ji dadin wannan labari amma dai yakamata gwamnati ta duba a biya mu sauran ma da wasu alawus-alawus namu. Ba wai rashin godiyar Allah bane amma basussuka sun yi mana katutu.
“Kamar a bangarena ina da marayu a gabana, nice ke biyan kudin makarantarsu da duk wani nauyi nasu. Ba karamin tashin hankali da damuwa na shiga ba a lokacin da aka ki biyanmu albashin watannin nan, yanzu ne nake kan farfadowa don dai ban gama warware basussukan mutane da suka taru a kaina ba.”

Majalisar tarayya ta bukaci a kara wa malaman firamare, sakandire da jami'o'i albashi

A wani labarin kuma, mun ji cewa kwamitin Majalisar Wakilai Tarayya kan Ilimin Jami'o'i ya yi kira da a kara albashi ga malaman makarantun firamare da sakandare da na jami'o'i.

Kwamitin ya ce kamata ya yi a riƙa biyan malaman Firamare N250,000, Malaman Sakandire N500,000 yayin da Malaman jami'a su riƙa samun miliyan ɗaya a matsayin albashi duk wata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel