Mutane Da Dama Sun Jikkata Yayin da Magoya Bayan APC Da SDP Suka Kara Gabannin Zaben Gwamnan Kogi

Mutane Da Dama Sun Jikkata Yayin da Magoya Bayan APC Da SDP Suka Kara Gabannin Zaben Gwamnan Kogi

  • Magoya bayan jam'iyyar APC da SDP sun yi kazamin karo gabannin zaben gwamnan jihar Kogi da za a yi a ranar 11 ga watan Nuwamba
  • An yi karon ne a karamar hukumar Idah inda magoya bayan jam'iyyun biyu suka yi musayar wuta
  • Wani jami'in dan sanda da wasu mutum hudu sun jikkata yayin da aka lalata wasu motoci a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba

Jihar Kogi - An samu hatsaniya a yankin karamar hukumar Idah ta jihar Kogi yayin da magoya bayan jam'iyyar APC da SDP suka yi musayar wuta.

Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, mutane da dama sun jikkata a rikicin wanda ya afku a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba.

An yi karo tsakanin magoya bayan APC da SDP
Mutane Da Dama Sun Jikkata Yayin da Magoya Bayan APC Da SDP Suka Kara Gabannin Zaben Gwamnan Kogi Hoto: @OfficialOAU/@Theta
Asali: Twitter

An tattaro cewa wani jami'in dan sanda da wasu sun ji rauni sakamakon harbi da aka yi sannan an lalata motoci.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Yi Kwantan Ɓauna, Sun Kai Hari Kan Ayarin Ɗan Takarar Gwamna a Jihar Arewa

Kakakin yan sandan jihar, SP William Aya, ya tabbatar da faruwar lamarin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, 19 ga watan Oktoba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aya ya bayyana cewa kwamishinan yan sandan jihar, CP Bethrand Onuoha ya yi umurnin gudanar da bincike a kan lamarin.

Ya kuma gargadi masu tada zaune tsaye gabannin zaben gwamnan na ranar 11 ga watan Nuwamba a jihar.

Ya ce:

"Kwamishinan ya sake nanata aniyar rundunar na ci gaba da jan hankalin masu ruwa da tsaki a harkokin tsaro na zabe don tabbatar da ingantaccentsaro a tsarin zaben.
“Rundunar a shirye take don ba dukkan Jam’iyyun siyasa damar gwabzawa yayin da suke gudanar da yakin neman zabe, gangami, tattaki da sauransu.”

Jam'iyyar SDP ta zargi APC da daukar nauyin yan daba domin su mamaye gangaminta da kuma fatattakar magoya bayanta a Ejule Kogi, karamar hukumar Ofu, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Kai Kazamin Hari Wata Jihar Arewa, Sun Halaka Mutum 2 Da Sace Wasu 3

Zaben Kogi: Dino Melaye ya tona asirin Gwamna Yahaya Bello na zarce wa zango na uku

A wani labarin, dan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP a zaben jihar Kogi mai zuwa ranar 11 ga watan Nuwamba, Dino Melaye, ya tona muhimmin abu game da Gwamna Yahaya Bello.

Sanata Dino Melaye ya yi zargin cewa Gwamna mai ci na jihar Kogi, Yahaya Bello, na ƙoƙarin ta zarce zango na uku a kan mulki ta hanyar kafa wakili. R

Gwamna Bello, wanda ke a siraɗin ƙarshe na zangon mulkinsa na biyu, yana goyon bayan ɗan takarar jam'iyyarsa ta APC, Usman Ododo, a zaɓen watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel