Tinubu Ya Nada Shaakaa Chira a Matsayin Sabon Mai Binciken Kudi Na Kasa

Tinubu Ya Nada Shaakaa Chira a Matsayin Sabon Mai Binciken Kudi Na Kasa

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake sabon nadi mai muhimmanci a gwamnatinsa
  • Tinubu ya nada Mista Shaakaa Chira domin ya zama sabon babban mai binciken kudi na kasa
  • Chira shine ya zama zakaran gwajin dafi a jarrabawar da dukkanin masu neman kujerar kamar yadda hukumar kula da ma'aikatan gwamnatin tarayya ta bayyana

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Tinubu ya zabi Mista Shaakaa Chira a matsayin sabon babban mai binciken kudi na kasa (AGF).

Wannan nadin ya biyo bayan nasarar tantance Mista Chira da hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya (FCSC) ta yi, inda ta ayyana shi a matsayin wanda ya fi cancanta.

Shugaban kasa Bola Tinubu ya nada sabon babban mai bincike na kasa
Tinubu Ya Nada Shaakaa Chira a Matsayin Sabon Mai Binciken Kudi Na Kasa Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Nadin na kunshe ne a cikin wata sanarwada mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin labarai, Ajuri Ngelale, ya saki, rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

Shetty, El-Rufai da Sauran Mutum 5 da Tinubu Ya Ba Mukamai, Sai Ya Dawo Ya Karbe

Shugaban kasa Tinubu, ya nuna karfin gwiwarsa a kan Mista Chira, yana mai sa ran cewa zai kiyaye manyan tsare-tsare da kuma cika abin da yan Najeriya ke tsammani kamar yadda gwamnatin ta bayyana a ajandarta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce:

“Da karfin ikon da sashe na 86 na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka gyara) ya ba shi, Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nadin Mista Shaakaa Chira a matsayin babban mai binciken kudi na kasa, bisa shawarar da Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin ta Tarayya (FCSC) ta bayar.
“Shugaban kasar ya amince da nadin Mista Chira ne bayan da hukumar kula da ma’aikatan gwamnatin tarayya (FCSC) ta gudanar da aikin tantancewa wanda ya bayyana Mista Chira a matsayin wanda ya fi kowa cancanta kuma ya yi nasarar samun maki mafi yawa a cikin dukkanin mutanen da suka zana jarrabawar nemam kujerar."

Kara karanta wannan

Gumi: Wike Shedanin Mutum Ne, Za Mu Saka Kafar Wando Daya Da Tinubu Idan Bai Cire Shi Ba

Yajin aikin ASUU: Tinubu ya bada umurnin a biya lakcarori albashinsu da aka rike

A wani labarin, mun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince a biya albashin watanni hudu da aka rikewa malaman jami’o’i karkashin kungiyar ASUU.

Hakan ya biyo bayan jingine tsarin "ba aiki, ba biya" da aka kakabawa malaman ASUU kan shafe tsawon watanni takwas suna yajin aiki a 2022, jaridar The Nation ta rahoto.

Mai ba shugaban kasa shawara ta musamman kan harkokin labarai, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, 20 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel