Manyan Labarai A Yau
Mutane su na ta tofa albarkacin bakinsu ganin yadda ake ta ruwan mukamai ba. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cigaba da nade-naden mukamai a gwamnatinsa.
Jami'an tsaro na ƴan sakai sun samu nasarar halaka masu garkuwa da mutane mutum huɗu a wani artabu da suka yi a jihar Kebbi bayan sun kai musu sumame.
Hukumar INEC ta bayyana matsayinta a kan sakamakon zaben da ke yawo wanda Dino Melaye da Murtala Ajaka, yan takarar PDP da SDP a zaben Kogi suka yada.
Akalla ciyamomin kananan hukumomi shida na jam’iyyar LP ne suka yi watsi da dan takararsu na gwamna a jihar Bayela, sun bayyana dalilinsu a ranar jajiberin zaben.
Jami'an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), sun kasa samun motocin da za su yi jigilarsu zuwa rumfunan zaɓe, a zaɓen gwamnan jihar Kogi.
Hukumomin sojojin Najeriya sun kama wasu mutane a cikin wasu bakaken motoci da ake zargin za su kawo hargitsi ne a jihar Kogi yayin da aka fara zabe.
Rahotannin da ke fitowa sun tabbatar ɓarkewar rikici a ƙauyen Agudama-Ekpetiama a jihar Bayelsa yayin da jami'an INEC suka tsere domin tsira da ransu.
Hukumar yan sandan Najeriya ta yi zargin cewa wasu yan siyasa sun dau hayar yan baranda a matsayin jami’an tsaro don tarwatsa zaben gwamna a Bayelsa.
A wani zaɓen jin ra'ayi da Legit.ng ta gudanar a Twitter, mutane mafiya yawa da suka bayyana ra'ayinsu a zaɓen, sun yi hasashen Dino Melaye zai yi nasara.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari