Manyan Labarai A Yau
Rabaran Mathew Kukah, ya bayyana a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, cewa sukar gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da yake yi ba wai na kashin kai bane.
Jama’a sun yi cece-kuce bayan barambaramar da Usman Ododo, dan takarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Kogi ya yi. Ya kira kansa a matsayin mace.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya sha alwashin ganin bayan ƴan bindigan da suka addabi jiharsa da kai hare-hare kan mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba.
Wata matashiya yar Najeriya ta fallasa wani faston bogi bayan ya ki bata cikon kudinta N100k. Budurwar ta yi karyar kurumta a shirin mu’ujiza na bogi.
Ƴan ta'addan Boko Haram sun dasa bam a jihar Borno wanda ya yi sanadiyyar salwantar da rayukan wasu manyan kwamandojin CJTF guda biyu da wasu mutum huɗu.
Yaƙin da Isra'ila ta ƙaddamar a kan Falasɗinu ya shafe fiye da wata ɗaya ana gwabzawa. Akwai ƙasashen da ke goyon bayan Isra'ila duk da kashe-kashen da ta ke yi.
Jigon jam'iyyar APC mara lafiya Frank Kokori ya koka kan yadda ciwonsa ya tu tsanani kuma ya kasa samun taimako domin ya yi jinyar yadda ya da ce.
Mambobin kungiyar NLC da TUC sun tattara kansu don gudanar da zanga-zanga a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja a ranar Alhamis, 9 ga watan Nuwamba.
Farashin gangar danyen mai na Brent ya karye zuwa $80 a kasuwar duniya. Najeriya da aka dogara da mai domin samun kudin shiga ba za su ji dadin labarin ba
Manyan Labarai A Yau
Samu kari