Zaben Bayelsa: Yan Sanda Sun Bankado Shirin Yan Siyasa Na Tarwatsa Zaben da Jami’an Tsaro Na Bogi

Zaben Bayelsa: Yan Sanda Sun Bankado Shirin Yan Siyasa Na Tarwatsa Zaben da Jami’an Tsaro Na Bogi

  • Hukumar yan sanda ta bankado wani kulla-kulla da yan siyasa ke yi don kawo karan tsaye a zaben gwamnan jihar Bayelsa
  • DIG Daniel Sokari-Pedro ya yi zargin cewa yan siyasa sun dauki hayar wasu jami'an tsaro na bogi to hargitsa zaben
  • Sai dai, ya sha alwashin tsamo wadannan yan baranda tare da gurfanar da su a gaban doka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Bayelsa - Rundunar yan sandan ta bayyana aniyar ta na fatattakar jami’an tsaro na bogi da yan siyasa suka baza domin kawo cikas a zaben gwamnan Bayelsa a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamba.

Daniel Sokari-Pedro, Mataimakin Sufeto Janar na yan sanda (DIG) mai kula da Kudu-maso-kudu, ya bayyana wa manema labarai a Yenagoa a ranar Juma’a, 10 ga Nuwamba, cewa yan sanda za su yi taka-tsantsan wajen zakulo wadannan jami’an tsaro na bogi.

Kara karanta wannan

Zaben gwamnan Imo 2023: Yan Najeriya sun yi hasashen wanda zai samu nasara

Rundunar yan sanda ta bankado masu shirin kawo cikas a zaben gwamnan Bayelsa
Zaben Bayelsa: Yan Sanda Sun Gano Sabon Yunkuri da Ake Na Tarwatsa Zaben da Jami’an Tsaro Na Bogi Hoto: The Nigerian Police
Asali: Facebook

Ya jaddada cewar manufar irin wadannan yan siyasa shi ne su haifar da tashin hankali da hargitsa yayin zaben.

Ana kyautata zaton sanarwar da yan sandan ta yi yana da nasaba da rahotannin da ke nuni da cewa wasu yan siyasa sun cika tsageru da kayan inifam din sojoji domin su yi katsalandan a zaben kamar yadda Premium Times ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukumar yan sanda ta bayyana hukuncin da za a yanke wa wadanda suka aikata laifin zabe

Sokari-Pedro ya tabbatar da cewa mutanen da aka kama a kan wadannan ayyukan za su fuskanci mummunan hukunci sannan a gurfanar da su a gaban kotu.

Ya ce:
“Ina mai tabbatar maku cewa ko da irin wadannan jami’an tsaro na karya ne ko na gaske, idan aka kama su, suna cikin babbar matsala.
"Za su yi danasanin ranar da aka haifo su a duniyar nan, ina mai ba su tabbaci.

Kara karanta wannan

Kogi: Dino Melaye ya lissafa jerin sunayen yan siyasa da ske son kashewa

"Imma su na bogi ne ko na gaske, matsalar ita ce cewa suna hargitsa tsarin zaben."

DIG din ya kuma gargadi yan siyasa da su guji furta kalaman tunzura jama’a da ka iya ta’azzara halin da ake ciki a Bayelsa kafin zaben.

Ya kuma bukaci wadannan yan siyasa da su guji kalaman raba kan jama’a, yana mai jaddada cewa yan sanda da sauran jami’an tsaro za su dauki mataki a kan duk wani mai kokarin kawo cikas ga zaman lafiyar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel