Zaɓen Kogi: Jami’an INEC Sun Maƙale, Sun Rasa Motocin Zuwa Rumfunan Zaɓe, Hotuna Sun Bayyana

Zaɓen Kogi: Jami’an INEC Sun Maƙale, Sun Rasa Motocin Zuwa Rumfunan Zaɓe, Hotuna Sun Bayyana

  • An samu tsaiko wajen fara.gudanar da zaɓen gwamnan jihar Kogi na ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023
  • Wannan tsaikon ya samu ne sakamakon rashin samun motocin hawa da za su yi jigilar jami'an INEC zuwa rumfunan zaɓe
  • Sama da jami'an hukumar 200 ne suka maƙale a birnin Lokoja suna jiran motocin da za su kai su rumfunan zaɓe

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kogi - An fara zaɓen gwamnan jihar Kogi ba da ƙafar dama ba, yayin da jami'an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), suka rasa motocin da za su yi jigilarsu zuwa rumfunan zaɓe.

Kamar yadda jaridar The Punch ta rahoto, jami’an hukumar ta INEC da aka tura rumfunan zaɓe daban-daban a faɗin birnin Lokoja suna maƙale a makarantar tunawa da Ajayi Crowther.

Kara karanta wannan

Bayelsa: "Dole a dakatar da zaɓukan da ake yi bayan babban zabe" Tsohon shugaban ƙasa ya faɗi dalili

Zaɓe ya tsaya cak a Kogi
Jami'an INEC a Kogi sun kasa samun motocin zuwa rumfunan zaɓe Hoto: Deborah Tolu-Kolawole
Asali: Twitter

Jami’an sun kasance a wurin domin karɓar kayayyakin zaɓen da za a gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami'an INEC sun rasa motoci

Daga cikinsu akwai ƴan bautar ƙasa da ma’aikatan wucin gadi da hukumar ta ɗauko domin gudanar da zaɓen.

Duk da cewa jami'an sun karɓi kayayyakin zaɓen, har yanzu suna nan a maƙale saboda babu wata motar da za ta yi jigilarsu zuwa rumfunan zaɓe.

An ji wani jami’i yana sanar da wasu jami’an cewa hanya ɗaya tilo da za su iya zuwa rumfunan zaɓensu, su ita ce idan masu kada ƙuri’a a rumfunan zaɓe sun samar musu da motocin da za su yi jigilarsu.

Ya zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, lananan motocin bas guda uku ne kawai aka gani a wajen don jigilar jami'an zaɓe sama da 200.

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke wajen zaɓe a Bayelsa yayin da jami'an INEC suka nemi tsira da ransu, bidiyo ya fito

Sojoji Sun Cafke Motoci 3 a Kogi

A wani labarin kuma, dakarun sojoji masu aiki na musamman domin zaɓen jihar Kogi sun cafke wasu baƙaƙen motoci guda uku.

Sojojin sun cafke baƙaƙen motocin ne saboda ba a san daga ina suke ba kuma akwai alamun tambaya a kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel