Subhanallahi: Rayukan Mutum 8 Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota

Subhanallahi: Rayukan Mutum 8 Sun Salwanta a Wani Mummunan Hatsarin Mota

  • An samu aukuwar wani mummunan hatsarin mota a jihar wanda ya yi sanadiyyar rasuwar mutum takwas
  • Hukumar FRSC wacce ta tabbatar da aukuwar hatsarin ta ce wasu mutum shida sun samu raunuka a hatsarin
  • Hukumar ta yi bayanin cewa hatsarin ya auku ne bayan wata motar bas ta yi taho mu gama da wata motar tirela

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kwara - Mutum takwas sun rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya auku a Oke Onigbin, kusa da hanyar Omu-Aran-Ilorin cikin ƙaramar hukumar Irepodun a jihar Kwara a yammacin ranar Juma’a.

Kwamandan hukumar kiyaye haɗura ta ƙasa (FRSC) a jihar Stephen Dawulung, ya tabbatar da rasuwar ta cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, SRC Busari Basambo, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Jiragen yakin rundunar sojojin sama sun halaka kasurgumin shugaban yan ta'addan Boko Haram

Mutum 8 sun mutu a hatsarin mota a Kwara
Rayukan mutum 8 sun salwanta sakamakon hatsarin mota a Kwara Hoto: FRSC, Nigeria
Asali: UGC

Yadda hatsarin motan ya auku

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mummunan hatsarin mota ya auku a yammacin ranar Juma’a, a Oke Onigbin, kan titin Omu-Aran-Ilorin, ƙaramar hukumar Irepodun ta jihar Kwara, da ƙarfe 7:40 na dare."
"Hatsarin ya haɗa da wata motar tirela ƙirar Mack da wata motar bas ƙirar Mitsubishi.

Kwamanda Dawulung ya ce, nan take bayan sun samu rahoton aukuwar hatsarin, tawagar ceto ta FRSC da ke a Omuaran suka garzaya wurin, domin ceto, rahoton Tribune ya tabbatar.

A kalamansa:

"Bincike na farko da mutanen mu suka yi ya nuna cewa motar ƙirar Mitsubishi (mai tafiya zuwa Ilorin) a lokacin da ta wuce wata motar bas, ta yi karo da wata motar Mack Trailer da ke tahowa."
"Lamarin ya yi sanadiyar mutuwar mutum takwas nan take, babban namiji ɗaya, manyan mata uku da yara huɗu, yayin da wasu mutum shida suka samu raunuka daban-daban."

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yan bindiga sun buɗe wuta, sun yi garkuwa da shugaban APC a jihar arewa

Kwamandan sashin ya ce an kai waɗanda hatsarin ya ritsa da su zuwa asibitin Ajisafe Omuaran domin kula da lafiyarsu, yayin da aka ajiye gawarwakin mutum takwas a dakin ajiye gawa na asibitin Adeyemo, Omuaran.

Ya ce, binciken da aka yi ya nuna cewa hatsarin ya auku ne sakamakon gudun da ya wuce ƙa'ida, wucewar da ba ta dace ba da kuma rashin gani.

Mutum Huɗu Sun Rasu a Hatsarin Mota

A wani labarin kuma, wani mummunan hatsarin mota da ya auku a ƙaramar hukumar Takai ta jihar Kano, ya yi sanadiyyar rasuwar mutum huɗu.

Mutane da dama sun kuma samu raunuka a hatsarin motan wanda ya auku a kan titin Dinyar Madiga a ƙaramar hukumar ta Takai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel