Dakarun Sojoji Sun Fatattaki Yan Bindiga a Jihar Arewa, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace

Dakarun Sojoji Sun Fatattaki Yan Bindiga a Jihar Arewa, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace

  • Dakarun sojojin Najeriya tare da haɗin gwiwar ƴan sakai sun samu galaba kan ƴan bindigan da suka addabi bayin Allaj a jihar Kebbi
  • Dakarun sojojin sun kai sumame a maɓoyar ƴan bindigan da ke a Tsaunin Damisa cikin ƙaramar hukumar Shanga ta jihar
  • A yayin sumamen da dakarun sojojin suka kai, sun samu nasarar fatattakar ƴan bindigan tare da ceto mutum shida da suka sace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kebbi - Dakarun rundunar sojojin Najeriya da ƴan sakai sun ceto wasu mutum shida da ƴan bindiga suka yi garkuwa da su a jihar Kebbi.

Jami'an tsaron sun samu nasarar ceto mutanen ne a dajin da ke ƙaramar hukumar Shanga ta jihar Kebbi a ranar Juma'a, 24 ga watan Nuwamba, cewar rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Jiragen yakin rundunar sojojin sama sun halaka kasurgumin shugaban yan ta'addan Boko Haram

Dakarun sojoji sun ceto mutum shida a Kebbi
Dakarun sojoji sun ceto mutum 6 da yan bindiga suka sace a Kebbi Hoto: Nigerian Army
Asali: Twitter

Malam Yahaya Sarki, mai ba Gwamna Nasir Idris shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama'a ne ya bayyana hakan a Birnin Kebbi a ranar Asabar, 25 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda sojojin suka kuɓutar da mutanen

Malam Yahaya ya bayyana cewa an kuɓutar da dukkanin mazan da aka yi garkuwa da su cikin ƙoshin lafiya kuma an miƙa su hannun iyalansu.

A kalamansa:

"Dakarun bataliya ta ɗaya da ke barikin Dukku, a Birnin Kebbi tare da ƴan sakai sun kai farmaki tsaunin Kogon Damisa da ke kusa da Saminaka a ƙaramar hukumar Shanga, garin da ke kan iyaka tsakanin Kebbi da Neja a ranar Juma'a"
"Rundunar ta fatattaki ƴan bindiga da dama tare da ceto mutum shida da aka yi garkuwa da su."
"Mutanen da abin ya shafe an riga da an bayar da rahoton ɓacewarsu, yayin da aka sace su da dadewa."

Kara karanta wannan

Luguden wuta: Sojoji sun kai samame maɓoyar yan bindiga a garuruwa 6, da yawa sun sheka lahira

Sarki ya yabawa kwazon sojojin tare da jaddada kuɗirin gwamnati na tallafawa hukumomin tsaro a jihar.

Dakarun Sojojin Sama Sun Halaka Mayakan Boko Haram

A wani labarin kuma, dakarun sojojin saman Najeriya sun kai hare-hare ta sama kan maɓoyar ƴan ta'addan Boko Haram a tsaunin Mandara da ke jihar Borno.

Hare-haren da dakarun sojojin suka kai ya yi sanadiyyar salwantar da rayukan wani babban shugaban ƴan ta'ddan da mayaƙa masu yawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel