Jiragen Yakin Rundunar Sojojin Sama Sun Halaka Kasurgumin Shugaban Yan Ta'addan Boko Haram

Jiragen Yakin Rundunar Sojojin Sama Sun Halaka Kasurgumin Shugaban Yan Ta'addan Boko Haram

  • Wani ƙasurgumin shugaban ƴan ta'addan Boko Haram ya baƙunci lahira a wani harin dakarun sojojin sama
  • Jiragen rundunar sojojin saman sun yi luguden wuta ne a maɓoyar ƴan ta'addan da ke a tsaunin Mandara na jihar Borno
  • Bayan ƙasurgumin shugaban ƴan ta'addan da aka halaka, an kuma halaka mayaƙan ƙungiyar masu tarin yawa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Dakarun rundunar sojin sama na Operation Hadin Kai, sun halaka wani ƙasurgumin shugaban ƴan ta'addan Boko Haram, Abu Asad da wasu da dama a harin da ta kai ta sama a maɓoyarsu da ke Tagoshe a tsaunin Mandara a Borno.

Daraktan hulda da jama’a da yaɗa labarai na rundunar sojojin saman Najeriya, Edward Gabkwet ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar a Abuja.

Kara karanta wannan

Luguden wuta: Sojoji sun kai samame maɓoyar yan bindiga a garuruwa 6, da yawa sun sheka lahira

Rundunar sojojin sama sun kashe shugaban yan ta'addan Boko Haram
Kasurgumin shugaban yan ta'addan Boko Haram ya halaka a harin sojojin sama Hoto: Nigerian Airforce
Asali: Twitter

Gabkwet ya ce hare-haren da aka kai ta sama da aka gudanar a ranar Juma'a na ɗaya daga cikin hare-haren da rundunar sojin sama ta Operation Hadin Kai ta kai a baya bayan nan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce rundunar sojin saman ta gano tarin ƴan ta’adda a wani waje da ke ɗauke da wasu gine-gine guda uku da ke cikin bishiyoyi.

Ya ƙara da cewa a bayyane yake a cikin faifan bidiyon cewa ƴan ta'addan sun haɗu a wajen ne domin yin taro ko kitsa wani gagarumin hari kan dakarun sojoji.

Ƴam ta'adda da dama sun halaka

A cewarsa, sama da ƴan ta’adda 100 ɗauke da muggan makamai aka gani suna ta harkokinsu a wajen wanda yake ɗauke motoci huɗu.

A kalamansa:

"Bayanan harin da aka kai ta sama ya nuna cewa an lalata biyu daga cikin gine-ginen uku, da kuma ɗaukacin motocin da ke wajen."

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun dauki mataki mai tsauri kan masu ba yan bindiga bayanai a jihar Arewa

"Akwai kuma alamun Abu Asad, jigo a tawagar Ali Ngulde ta Boko Haram, da kuma sauran ƴan ta’adda irin su Ibrahim Nakeeb, Mujaheed Dimtu, Mustafa Munzir da mayaƙa da dama na daga cikin ƴan ta’addan da aka halaka su a harin ta sama."

Sojoji Sun Yi Ruwan Muta a Maɓoyar Ɗan Boko Haram

A wani labarin kuma, an kashe ‘yan ta’adda da dama a wani samame da rundunar sojin sama ta Operation Whirl Punch ta kai a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Sojojin sun kai harin ne bayan wani rahoton sirri da rundunar ta samu na cewa wani dan ta'adda mai suna Boderi da mambobinsa sun yi mafaka a wurin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel