Manyan Labarai A Yau
Hukumar EFCC na cigaba da bincike kan badakalar N44bn da aka bankado a ma'aikatar jin kai da yaki da talauci. Hukumar ta fara bincikar bankuna uku.
Sanata Ali Ndume wanda ya yaba ma shugaban kasa Bola Tinubu kan dakatar da Betta Edu, ya yi gagarumin gargadi a kan barayin yan siyasa masu tasowa.
Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta kama kimanin kwalaben giya iri-iri 850 a karamar hukumar Kankara. Kwamandan hukumar, Aminu Usman ne ya jagoranci aikin.
Kungiyoyin mata a jihar Yobe sun gudanar da zanga-zanga kan kisan wata matar aure mai suna Ammi Adamu Mamman, da ake zargin mijinta ya yi Damaturu.
Shehu Sani ya yaba ma Shugaban kasa Bola Tinubu kan daukar matakin gaggawa a takkadamar ministar jin kai, Betta Edu, na badakalar kudi a ma’aikatarta.
Fadar shugaban kasa ta soke katin dakatacciyar ministar jin kai, Dr Betta Edu wanda shi ke ba ta damar shiga Villa. Wannan matakin zai hana ta ganin Tinubu.
Hukumar EFCC za ta yi wa Betta Edu tambayoyi a lokacin da ba a gama binciken Sadiya Umar-Farouk ba bayan tsohuwar ministar jin-kai ta ce ba ta da cikakken lafiya.
Shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi magana kan gwamnoni, sanatoci da yan majalisun da za su dawo APC.
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da dabararta don magance hauhawan farashin kayayyaki a fadin kasar, yayin da al’ummar Najeriya ke kara shiga damuwa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari