Badakalar N2.3tr: Betta Edu Za Tayi Gaba da Gaba da EFCC da Tinubu Ya Ajiye Sanayya

Badakalar N2.3tr: Betta Edu Za Tayi Gaba da Gaba da EFCC da Tinubu Ya Ajiye Sanayya

  • Bola Ahmed Tinubu ya umarci EFCC ta gudanar da bincike bayan ya dakatar da Betta Edu daga ofis
  • Ajuri Ngelale ya ce Mai girma Shugaban kasar ya sa a binciki zargin badakala a ma’aikatar jin kai
  • Hukumar EFCC za ta yi wa Edu tambayoyi a lokacin da ba a gama binciken Sadiya Umar-Farouk ba

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

AbujaShugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarni ga hukumar EFCC ta yi cikakken bincike a ma’aikatar jin kai da yaki da talauci.

Shugaban kasar ya sanar da haka ne a jawabin da Ajuri Ngelale ya fitar yayin da aka dakatar da Betta Edu game da zargin badakalar N585m.

Sadiya, Betta Edu
EFCC na binciken Sadiya Umar Farouk, Betta Edu, Halima Shehu Hoto: @Sadiya.Farouk, thenigerialawyer.com, medium
Asali: Twitter

Punch ta ce za ayi binciken ne daidai lokacin da tsohuwar ministar ma’aikatar, Sadiya Umar-Farouq ke hannun EFCC kan binciken N37.1bn.

Kara karanta wannan

EFCC ta sanar da matakin da za ta dauka da Godwin Emefiele ya yi nasara a kotu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC za ta binciki N2.3 a ma'aikatar jin-kai

Bayanan da aka samu daga ofishin kasafin kudi ya nuna an warewa tsohuwar ma’aikatar jin kai da kula da annoba N2.38tn daga 2020-2024.

A dalilin umarnin da shugaban kasa ya bada, EFCC a karkashin jagorancin Ola Olukoyede, ta aika takardar gayyata zuwa ga Dr. Betta Edu.

Yau EFCC za tayi wa Madam Betta Edu tambayoyi

Hukumar EFCC ta bukaci Betta Edu ta je gabanta a ranar Talata domin jami’ai su fara bincike.

A yau ake sa ran ma’aikatan hukumar yaki da rashin gaskiyar za su yi wa dakataciyyar ministar tambayoyi a babban ofishinta da ke Jabi.

Wani rahoton ya ce Edu ba ta iya mika ragamar ma’aikatarta ga babban sakatare kamar yadda shugaban kasa ya bada umarni a makon nan ba.

Sadiya Farouk da Edu a EFCC

Kara karanta wannan

Ba da ni ba: Minista Ya Fitar da Kan Shi Daga Zargin Karbar N438m a Hannun Betta Edu

NEDC, NCR, NAPTIP da hukumar da ke kula da ‘yan gudun hijira sun samu makudan biliyoyi daga cikin kason ma’aikatar a tsawon shekaru hudu.

A cikin wadanan kudi hukumar NEMA ta samu N4.03bn, hukumar NEDC ta tashi da N400bn

A kasafin kudin 2024, an warewa ma’aikatar tarayyar N426bn ne da farko, daga baya majalisa ta kara shi zuwa N532.5bn kamar yadda aka roka.

Jami'an EFCC v Halima Shehu

Rahoto ya zo kwanan baya cewa Hukumar EFCC ta yi caraf da Halima Shehu, wanda ita ce dakatacciyar shugabar hukumar NSIPA ta kasa.

Hukumar ta yi bayanin cewa Halima ta na da tambayoyin da za ta amsa kan badaƙalar N37bn, zuwa yanzu ana cigaba da bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel