Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Tinubu Ya Dakatar da Betta Edu, Ya Yi Shagube Ga Buhari

Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Tinubu Ya Dakatar da Betta Edu, Ya Yi Shagube Ga Buhari

  • Dakatar da Minista Betta Edu da Shugaban kasa Tinubu ya yi a kan badakalar kudi naira miliyan 585 ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
  • Da yake martani, Shehu Sani, ya bayyana cewa binciken EFCC ya aike da sako karara kan mahimmancin bin diddigi a gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Tinubu
  • Furucin Sani a dandalin X ya haddasa cece-kuce a tsakanin jama'a game da bambancin tsarin shugabancin Tinubu da na Buhari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya yi tsokaci kan dakatar da Betta Edu, ministar jin kai da kawar da talauci da aka yi.

Ku tuna cewa a ranar Litinin, 8 ga watan Janairu, Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi umiurnin dakatar da ministar, Edu, kan badakalar kudi naira miliyan 585 a ma'aikatarta.

Kara karanta wannan

Awanni kadan bayan dakatar da ita, Ministar Tinubu ta sha kunya a fadar Aso Rock, an fadi dalili

Shehu Sani ya goyi bayan dakatar da Betta Edu
Shehu Sani Ya Yi Martani Yayin da Tinubu Ya Dakatar da Betta Edu, Ya Yi Shagube Ga Buhari Hoto: Shehu Sani, Dr Betta Edu
Asali: Facebook

A cewar sanarwa daga kakakin shugaban kasa Ajuri Ngelale, dakatarwar ya fara aiki nan take.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar Legit ta rahoto cewa badakalar sun hada da amincewa da biyan daruruwan miliyoyin naira cikin wasu asusu masu zaman kansu na ma'aikatan gwamnati.

Da yake martani ga ci gaban, wani rubutu da Sani ya wallafa a shafinsa na X (wanda aka fi sani da Twitter a baya) a ranar Litinin, ya yaba da matakin gaggawa da Shugaban kasa Tinubu ya dauka sannan ya yi shagube ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ya rubuta a shafin nasa:

"Wannan shugaban kasan ya saurari koken jama'a sannan ya dauki mataki a kan ministarsa. Idan da tsohon shugaban kasa ne sai dai kawai ya ba ku tabbaci."

Jama'a sun yi martani kan furucin Sani

@mamatii001 ta rubuta:

"Na ga dalilin da yasa ka samu kuri'u 2 a zaben fidda dan takarar gwamnan PDP tsohon sanata na. Baka da kirki."

Kara karanta wannan

Betta Edu: Jerin Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da Ministar da Tinubu ta dakatar

@MbanugoClement2 ya ce:

"Idan da tsohon ne, da zuwa yanzu ba zai sani ba duk da koken jama'a."

@FaithSuzy1 ta ce:

"Shugaban kasar na neman halacci ne, don haka ya dauki mataki kan ministarsa saboda wannan dalili."

An janye katin Betta Edu na Villa

A gefe guda, mun ji cewa ana ci gaba da fafatawa yayin da fadar shugaban kasa ta janye katin dakatacciyar ministar jin kai da kawar da talauci, Dr Betta Edu, wanda hakan zai hana ta shiga fadar villa da ke Abuja.

Awanni bayan dakatar da ita, fadar shugaban kasa ta toshe kafar da Edu za ta gana da Shugaban kasa Tinubu a Villa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel