Ana Tsaka da Binciken Betta Edu, Shugaban EFCC Ya Aike da Sabon Gargadi

Ana Tsaka da Binciken Betta Edu, Shugaban EFCC Ya Aike da Sabon Gargadi

  • Shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) ya aike da sabon gargaɗi ga masu cin hanci da rashawa
  • Ola Olukoyode ya bayyana cewa babu wani sauran wurin ɓoyo ga masu aiƙata cin hanci da rashawa a ƙasar nan
  • Shugaban ya yi nuni da cewa babu wanda ya fi ƙarfin hukumar ta bincike shi da zarar ya aikata ba daidai ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa ta'annati (EFCC), Ola Olukoyode, ya ce babu wurin ɓuya ga masu aikata cin hanci da rashawa a ƙasar nan.

Shugaban ya yi wannan gargaɗin ne lokacin da ya karɓi baƙuncin takwaransa na hukumar yaƙi da rashawa ta ICPC, Dr. Musa Aliyu.

Kara karanta wannan

Betta Edu: EFCC ta titsiye shugabannin bankuna 3 kan badakalar N44bn, bayanai sun fito

Shugaban EFCC ya aike da sabon gargadi
Shugaban EFCC ya ja kunnen masu cin hanci da rashawa Hoto: @OfficialEFCC
Asali: Twitter

Gargaɗin na sa na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ke bincikar wasu manyan jami'an gwamnati kan zargin cin hanci da rashawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ranar Talatar da ta gabata ne shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayar da umarnin dakatarwa da bincikar Halima Shehu, shugabar hukumar kula da jindaɗin al'umma ta ƙasa (NSIPA), bisa zargin almundahanar kuɗaɗe.

Hukumar EFCC ta kuma binciki tsohuwar ministar jinƙai da yaƙi da talauci, Sadiya Umar-Farouk bisa zargin almundahanar N37.1bn, da wacce ta gaje ta Betta Edu kan badaƙalar N586m.

Wane gargaɗi shugaban EFCC ya yi?

A kalamansa:

“Mun yi imanin cewa da irin shugaban da muke da shi, wanda a shirye yake kuma yake da niyyar yin abin da ya dace, kuma daga abin da muka gani a baya-bayan nan cikon sa’o’i 48 da suka gabata, a fili yake cewa ya samar da yadda zamu ji daɗin yin aiki.

Kara karanta wannan

Badakalar N438m: Minista ya magantu bayan Tinubu ya kira shi zuwa Villa, bayanai sun fito

"Don haka babu wurin fakewa ga masu cin hanci. Dole ne mu yi iya bakin ƙoƙarin mu, dole ne mu jajirce kuma mu baiwa shugaban ƙasa goyon bayan da yake buƙata. Babu wanda ya fi ƙarfin a bincike shi a ƙasar nan. Da zarar ka karya doka, za mu bincike ka."

EFCC Ta Fara Bincikar Bankuna 3

Rahoto ya zo cewa hukumar EFCC ta yi wa shugabannin bankunan Zenith, Providus da Jaiz tambayoyi kan badaƙalar N44bn.

Hukumar ta titsiye shugabannin bankunan ne yayin da take cigaba da bincike kan badaƙalar karkatar da kuɗaɗen da aka yi a ma'aikatar jin ƙai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel