Matashi Ya Yi Nadama Bayan Sayar da Gidansa Don Burge Budurwarsa, Ta Yi Masa Abin da Bai Yi Zato Ba

Matashi Ya Yi Nadama Bayan Sayar da Gidansa Don Burge Budurwarsa, Ta Yi Masa Abin da Bai Yi Zato Ba

  • Wani mutum a shafin X kwanan nan ya bayyana yadda ya sayar da gidansa a Lugbe don faranta wa tsohuwar budurwarsa wacce ba ta son unguwar
  • Sai dai kash, ba zato ba tsammani dangantakarsu ta zo ƙarshe, inda ya koma baya da gida a birnin tarayya Abuja
  • Masu amfani da yanar gizo sun bayyana kaɗuwarsu da matakin nasa tare da bayyana hakan a matsayin sakarci saboda ruɗin soyayyya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Wani ɗan Najeriya ya ba da labarin yadda ya yi asarar gidansa mai ɗakuna uku a Lugbe, cikin babban birnin tarayya Abuja.

A kullum tsohuwar budurwar tasa tana nuna masa rashin gamsuwa da unguwar, wanda hakan ya sanya shi yanke shawarar sayar da gidan don faranta mata rai.

Kara karanta wannan

"Burin kowane ɗan Najeriya ya ɗauki hoto da ni" Ministan Tinubu ya yi magana mai jan hankali

Matashi ya sayar da gidansa saboda budurwa
Matashi ya yi nadamar sayar da gidansa don burge budurwa Hoto: Issa Bin Saleh AlKindy, David Papazian/ Getty Images (Hoton an yi amfani da shi ne kawai don misali)
Asali: Getty Images

Matashi ya sadaukar da gidansa don soyayya

A cikin nuna soyayya da neman sasanci, mutumin wanda yake amfani da sunan @JasonNotJerulo akan shafin X, ya sadaukar da gidansa saboda soyayyar su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin takaici, duk da sadaukarwar da ya yi, soyayyar ta su ta zo ƙarshe.

Sakamakon haka Jason ya tsinci kansa ba gida a Abuja, inda ya yi nadamar sayar da kadarorinsa.

Rashin gidan nasa ya sa ya yi ta tunani a kan yadda soyayya ka iya sanya mutum ya yi abin da baya da niyya, da illar fifita abin da wani ke so fiye da wanda mutum yake so.

A kalamansa:

"Lokacin da nake zaune a Abuja ina da gida mai daƙuna uku da ke Lugbe. Tsohuwar budurwa ta sai ta riƙa ƙorafi akan wurin har na sayar da gidan don faranta mata rai. Yanzu mun rabu kuma ba ni da gida a Abuja. Wani lokaci soyayya wani makamin sanya ka yin abin da baka yi niyya ba ne.”

Kara karanta wannan

Sanata Ndume ya maida martani kan dakatar da ministar jin kai, ya aike da sako ga Tinubu

Masu amfani da yanar gizo sun mayar da martani

Da jin labarin Jason, masu amfani da yanar gizo sun bayyana mamakinsu kan shawarar da ya yanke.

Mutane da yawa sun ɗauke hakan a matsayin sakarci wanda ruɗin soyayya ya ja masa.

@Wizebaba ya rubuta:

"Kowace soyayya tana buƙatar lokaci, kawai ka ba ta lokaci."

@ThisisEazee ya rubuta:

"Kai daga mai gida zuwa mai haya saboda TOTO?? Shin Genevieve ce ita??"

@Sarauniya ta rubuta:

"A matsayina na mace na rantse maka Wallahi. Ka yi abun kunya."

@Irunnia_ ya rubuta:

"Bari na yarda cewa wannan wasa ne. Ba kowa ba ne zai yi wannan wawancin ba."

@47kasz ya rubuta:

"Dole ne wannan ya kasance wasa.. ba zai yiwu ka zama sakarai haka ba."

@talk2veee ta rubuta:

"Kada ka yarda mace ta ɗora ka akan hanyar rashin nasara. Idan ba ta sonka a yadda kake, gaya mata ta ba ka lokaci ko ta amince da kai a haka. Duk tsiya dai abin da za ta yi daga ƙarshe shi ne ta rabu da kai."

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi martani yayin da yan bindiga suka dawo titin Kaduna-Abuja, sun sace mutum 30

Matashi Ya Nemi Rabuwa da Budurwarsa da Suka Daɗe Tare

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani matashi ya yi yunƙurin rabuwa da budurwarsa da suka ƙwashe shekara bakwai tare.

Matashin dai ya yi mata tayin N5m domin ta rabu da shi ya samu ya auri wata daban ba ita ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel