Dakarun Sojoji Sun Ragargaji Yan Bindiga, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace a Jihar Arewa

Dakarun Sojoji Sun Ragargaji Yan Bindiga, Sun Ceto Mutanen da Suka Sace a Jihar Arewa

  • Dakarun sojoji sun samu nasarar yin galaba a kan miyagun masu garkuwa da mutane da suka sace fasinjoji tara a jihar Benue
  • Sojojin sun kuma ragargaji miyagun bayan sun yi musayar wuta da su tare da cafke mutum biyu daga cikinsu
  • A yayin samamen kuma da sojojin suka kai maɓoyar miyagun, sun kuma ƙwato makamai da wasu kayayyaki

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Dakarun rundunar 'Operation Whirl Stroke' (OPWS) tare da haɗin gwiwar ƴan sanda da sauran jami’an tsaro sun ceto mutum tara da aka yi garkuwa a jihar Benue.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa jami'an tsaron sun kuma samu nasarar cafke wasu mutum biyu da ake zargi.

Kara karanta wannan

Tsagerun ƴan bindiga sun yi garkuwa da basarake da wasu matasa uku a jihar arewa

Sojoji sun ceto mutanen da yan bindiga suka sace
Dakaru sojoji a Benue sun ceto mutanen da yan bindiga suka sace Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Kwamandan rundunar, OPWS, Manjo Janar Sunday Igbinomwanhia, ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Alhamis a Makurdi, babban birnin jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce sojoji sun ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su tare da cafke waɗanda ake zargin a wani samame da suka kai ranar Talata a dajin Owukpa da ke ƙaramar hukumar Ogbadibo a jihar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.

Igbinomwanhia ya ƙara da cewa waɗanda aka ceton sun haɗa da mata takwas da namiji guda ɗaya.

Yadda aka ceto mutanen

Ya ce samamen ya biyo bayan sace wasu fasinjoji da aka yi a cikin wata motar bas ta kasuwanci da ke kan titin Otukpo zuwa Enugu a ranar 11 ga watan Janairu.

A kalamansa:

“A yayin musayar wuta, masu garkuwa da mutanen sun tsere daga maɓoyarsu saboda luguden wutan da suka sha, inda suka bar mutanen a wurin.

Kara karanta wannan

Gwamna Makinde ya bayyana abin da ya haddasa tashin abin fashewa a Ibadan, bidiyo ya bayyana

"Wasu daga cikin kayayyakin da aka ƙwato a wurin sun haɗa da bindiga kirar AK 47 guda ɗaya da wayoyin hannu guda 10.
"Nan take aka garzaya da waɗanda aka ceto zuwa hedikwatar rundunar domin ba su agajin gaggawa.

Ya ƙara da cewa daga baya an bar mutanen da aka sacen su ci gaba da tafiyarsu zuwa garuruwansu bayan an yi musu jawabi.

Igbinomwahia ya ce an miƙa waɗanda ake zargin da duk wasu kayayyakin da aka ƙwato a yayin samamen ga ƴan sanda domin ɗaukar mataki na gaba.

Ƴan Bindiga Sun Nemi N50m Matsayin Kuɗin Fansa

A wani labarin kuma, kun ji cewa miyagun ƴan bindigan da suka sace shugaban ƙaramar hukumar Ukum a jihar Benue, sun buƙaci a ba su N50m a matsayin kuɗin fansa.

Ƴan bindigan dai sun yi awon gaba da shugaban ƙaramar hukumar ne lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa wajen jana'iza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng