Manyan Labarai A Yau
Mutanen wasu kauyukan jihar Zamfara sun shiga fargabar fuskantar hare-hare daga kasurgumin shugaban yan bindiga. Hakan ya sanya sun bar gidajensu.
A ranar Laraba, 17 ga watan Janairu, rundunar yan sandan Kano, ta ce ta kama mutum 5 kan haddasa rikici yayin murnar hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben jihar.
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, ya yi magana kan matsalar rashin tsaron da ake fama da ita, gwamnan ya yi nuni da cewa akwai sa hannun wasu jami'an tsaro.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba zai iya komawa Jamhuriyar Nijar ba saboda kulle iyakokin kasar nan.
Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta dage sauraron shari'ar da ake yi tsakanin wani mawakin Kano da BBC. Mawakin ya nemi BBC ta biya shi diyyar naira miliyan 120.
Jami'an tsaro sun yi nasarar dakile wani mummunan hari da tsagerun yan bindiga suka yi kokarin kaiwa al'ummar kauyen Tse Gaagum a yankin Logo dake jihar Benue.
Wata kungiyar arewa ta NEYGA ta yi alkawarin fallasa wadanda ke kokarin daure shugaban ma’aikatan Tinubu, Femi Gbajabiamila a binciken Betta Edu.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Cif Bisi Akande ya yi hasashen cewa yan siyasa masu tasowa za su fi na yanzu tafka barna da suka hada da rashawa.
An samu tashin gobara a babbar kasuwar Panteka da ke jihar Kaduna. Gobarar wacce ta tashi a cikin dare ta yi sanadiyyar asarar dukiya mai tarin yawa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari