Matashi Ya Gurfana a Kotu Kan Zargin Taba Muhibbar Malamin Addini a Kano

Matashi Ya Gurfana a Kotu Kan Zargin Taba Muhibbar Malamin Addini a Kano

  • Wani matashi mai suna Garzali Musa Obasanjo ya gurfana a gaban kotun shari'a da ke jihar Kano kan zargin taba muhibbar malamin addini
  • An dai zargi Musa Obasanjo da batanci da kuma cin mutuncin Sheikh Lawan Abubakar Triumph
  • Khadi na kotun musuluncin, Malam Abdullahi Halliru ya dage sauraron shari'ar zuwa ranar 13 ga watan gobe

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Kotun shari'ar addinin musulunci dake filin hoki a jihar Kano, ta dage ci gaba da sauraron shari'ar da ake yi tsakanin Sheikh Lawan Abubakar Triumph da Garzali Musa Obasanjo, zuwa ranar 13 ga watan Febrairu.

A zaman Kotun na yau Laraba, 17 ga watan Janairu, wanda wakilin Legit Hausa ya halarta, bangaren masu kara sun nemi kotun da ta basu wata ranar domin gabatar da shaidu kan wannan tuhuma ta batanci da cin mutunci, da ake yiwa Obasanjon.

Kara karanta wannan

Kotun Shari'ar Musulunci ta dauki sabon mataki kan shari'ar Idris Dutsen Tanshi, ta fadi dalilai

Matashi ya gurfana a kotu kan taba nuhibar Malam Triump
Matashi Ya Gurfana a Kotu Kan Zargin Taba Muhibbar Malamin Addini a Kano Hoto: Sheikh Lawan Abubakar Shu'aib Triumph
Asali: Facebook

Kan haka ne kuma alkalin kotun, Malam Abdullahi Halliru ya amince da wannan roko na masu karar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan fitowa daga kotun lauya mai kare wanda ake karar, Garzali Musa Obasanjo, Mukarram Umar Naseer, ya yiwa manema labarai karin bayani kan yadda zaman ya kasance a yau Laraba.

Umar Naseer ya ce:

“Eh to kamar yadda kuke gani mun shiga kotu a yau, kuma ka’idar shi ne fara saurarn hujjojin masu kara, kuma kamar yadda kuka ji sun nemi a dage sauraren shari’ar zuwa su tattara hujjojin.”
“Babban abin jira shi ne jiran ranar, su zo mana da hujjojin tabbatar da zargin da suke yi, ni kuma na kare domin wanda nake karewa bai aikata laifin da suke zarginsa da aikatawa ba.”

Muna fatan kotu za ta kwato mana hakkinmu, masu kara

Tunda farko dai shakikin malamin mai suna Muhammad Sani Abubakar ne ya shigar da karar Obasanjon a gaban 'yan sanda kan zargin batanci da taba muhibbar mahaifiyar Malam Lawan Triumph da 'yan uwansa a shafin sada zumunta.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama wasu mutane bayan hukuncin Kotun Koli a Kano, an samu karin bayani

Da yake ganawa da manema labarai ciki harda wakilin Legit jim kadan bayan kammala zaman kotun na yau, Abubakar ya ce suna fatan cewa kotun mai adalci za ta bi musu hakkinsu akan wanda suke karar wato Garzali Musa Obansanjo.

An soke lefe da kayan daki a Kano

A wani labari na daban, mun ji cewa a yayin da masu shirin yin aure ke kuka kan tilascin yin lefe a wannan tsadajjen lokaci, musamman ma matasa, wani lauya ya ce akwai dokar da ta hana yin lefe a jihar Kano.

Barista Abba Hikima ya ce akwai wata tsohuwar doka da aka samar tun zamanin mulkin sojoji, wacce ta haramta duk wasu tsarabe-tsarabe na aure da ba addini ne ya kawo su ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel