Gwamnan Sokoto Ya Shirya Samarwa Matasa Aikin Yi, Ya Yi Wata Hubbasa

Gwamnan Sokoto Ya Shirya Samarwa Matasa Aikin Yi, Ya Yi Wata Hubbasa

  • Gwamnatin jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu ta amince da sayo babura 1,000 domin samarwa da matasa aikin yi
  • Majalisar zartaswar jihar ce ta amince da hakan tare da ƙarin wasu keke Napep 500 a wani yunƙuri na ganin matasa sun samu abun dogaro da kai
  • Majalisar ta kuma amince da bayar da katin shaida ga ɗaliban makarantun sakandare na gwamnati da ke jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Sokoto - Majalisar zartaswar jihar Sokoto ta amince da sayen babura 1,000, tare da keke Napep 500, a wani ɓangare na shirin samarwa matasa aikin yi.

Hakan na daga cikin ƙudirin da aka cimma a ƙarshen taron majalisar zartarwa ta jiha da aka gudanar a zauren majalisar a ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

An samu barkewar wata cuta a Adamawa, mutum 42 sun rasa ransu

Gwamnan Sokoto zai saya babura
Gwamnatin Sokoto za ta samarwa matasa aikin yi Hoto: Ahmed Aliyu Sokoto
Asali: Facebook

Majalisar, a taron da gwamnan jihar Ahmed Aliyu Sokoto ya jagoranta, ta amince da bayar da katin shaida ga ɗaliban makarantun sakandaren gwamnati.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Za a ba ɗalibai katin shaida a Sokoto

Jaridar The Nation ta ce da yake zantawa da manema labarai a kan lamarin, kwamishinan ilimi na jihar, Tukur Arkali, ya bayyana cewa matakin ya zama dole saboda jihar na kashe makudan kuɗaɗe a jarabawar manyan makarantun sakandire.

"A bara kaɗai mun kashe N1bn kan jarabawowin NECO da WAEC ga ɗalibanmu."
"Kuma a bana, muna sa ran ɗalibai 33,000 da za su zauna jarabawar kuma da ƙarin kudin rajista da WAEC da NECO suka yi, za mu kashe kusan N1.9bn."

- Tukur Arkali

Majalisar ta kuma amince da gina magudanar ruwa a maƙabartar Tudun Wada, da kuma gyaran sansanin Hajji, wanda majalisar ta amince da sauya sunansa zuwa Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, tsohon gwamnan jihar.

Kara karanta wannan

Tudun Biri: Rundunar sojoji ta kammala bincike kan harin bam da ya hallaka masu Maulidi

Matsalar rashin ruwa a Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa kamfanoni da masu sana'ar da ke da alaƙa da ruwa sun shiga damuwa kan yadda rashin ruwa ke barazana ga ayyukansu a jihar Sokoto.

Hukumar samar da ruwan sha a jihar ce ta ɗauki matakin yanke ruwa ga kamfanonin a wurare da dama da ke cikin faɗin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel