An Harbi Wani Dan Jarida a Gidan Gwamnatin Kano, Bayanai Sun Fito

An Harbi Wani Dan Jarida a Gidan Gwamnatin Kano, Bayanai Sun Fito

  • Wani harsashi da ba a san daga inda ya fito ya dira a kan wani ɗan jarida a gidan gwamnatin jihar Kano inda ya yi masa rauni
  • Ɗan jaridar wanda yake aiki da gidan talabijin na Abubakar Rimi (ARTV) yana cikin harabar gidan gwamnatin ne lokacin da harsashin ya same shi
  • Ba a san daga inda harsashin ya fito ba yayin da ƴan sanda suka fara gudanar da binciken kan lamarin mai cike da ruɗani

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Wani ɗan jarida da ke aiki da gidan talabijin na Abubakar Rimi (ARTV) mallakin gwamnatin jihar Kano, Naziru Idris Ya’u, ya samu rauni daga wani baƙon harsashi a gidan gwamnati dake Kano.

Kara karanta wannan

Borno: Gwamna Zulum ya tafka babban rashi yayin da hadiminsa ya rasu

Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 3 ga watan Mayu, 2024, da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.

An harbi dan jarida a Kano
An harbi wani dan jarida a gidan gwamnatin Kano Hoto: Naziru Idris Ya'u
Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa wani gidan rediyo da ke Kano ne ya fitar da labarin aukuwar lamarin ranar Asabar da safe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Naziru yana zaune da abokansa a harabar gidan gwamnati, sai ya ji wani irin zafi a hannunsa. Da ya duba, sai ya ga harsashi a hannunsa, sai ya fahimci cewa an harbe shi.

Yadda lamarin ya auku

A kalamansa:

"Na ji wani abu ya bugi hannuna sai na ga harsashi ne. Da alama an harbo shi ne daga nesa."

Ya yi nasarar cire harsashin da kansa, sannan ba tare da ɓata lokaci ba aka kai shi asibitin gidan gwamnati domin kula da lafiyarsa.

Lamarin ya faru ne a ranar bikin ƴancin ƴan jarida ta duniya, wacce ake gudanarwa kowace shekara a ranar 3 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Digiri dan Kwatano: Gwamnatin tarayya ta juyo kan masu takardun bogi a Najeriya

Sai dai babu wanda ya ɗauki alhakin kai harin, kuma harsashin har ya zuwa yanzu ba a san daga inda ya fito ba, cewar rahoton The Punch.

Naziru ya bayyana cewa raunin da ya samu ƙarami ne, kuma ya samu kulawa a asibiti. Bayan an yi masa magani an sallame shi sannan aka bar shi ya koma gida.

Jami’an ƴan sanda da ke gidan gwamnatin sun ƙaddamar da bincike kan lamarin.

Kawo yanzu dai rundunar ƴan sandan jihar Kano da gwamnatin jihar ba su mayar da martani kan lamarin ba.

An tsinci gawar ɗaliba a Kano

A wani labarin kuma, kun ji cewa an tsinci gawar wata dalibar jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil, Aisha Yahaya, a wani gidan dalibai da ke wajen makarantar.

An tsinci gawar Aisha, ɗaliba ƴar aji 300 a fannin kimiya da fasahar abinci jim kaɗan bayan ta koma daƙinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel