Manyan Labarai A Yau
Wasu 'yan bindiga sun kai farmaki a jihar Kaduna inda suka tafka sabon ta'addanci. A yayin harin 'yan bindigan sun hallaka mutum shida tare da sace wasu da dama.
Fadar shugaban kasa ta yi martani ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, kan kalaman da ya yi dangane da siyo sabon jirgi ga Tinubu.
Wani Alhaji dan Najeriya ya rasu a kasa mai tsarki yayin gudanar da Hajjin bana saboda tsananin zafi. Alhajin ya rasu ne a kan hanyar zuwa jihar shaidan.
Alhaji Rabiu Musa Kwankwaso jagoran jam'iyyar NNPP kuma madugun Kwankwasiyya, ya yi zargin cewa makiyan jihar Kano na kokarin kawo hargitsi a jihar.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayyana cewa ko kadan bai damu ba kan binciken da majalisar dokokin jihar ke yi masa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya aika da sakon barka da Sallah ga shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu. Sakon na zuwa ne yayin da ake rikicin sarauta a jihar.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi karin haske kan rikicin masarautar Kano. Kwamishinan 'yan sanda a jihar ya ce sun samu umarnin kotu har guda biyar.
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi zargin cewa akwai shirin cafke magoya bayansa a jihar bayan sun fito sun nuna adawa da shugabannnin kananan hukumomi.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wani sojan Najeriya ya yanke shawarar raba kansa da duniya a jihar Abia. Sojan dai yana aiki ne da bataliya ta 144 a jihar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari