Rikicin Masarauta: Kwankwaso Ya Bayyana Masu Son Kawo Hargitsi a Kano

Rikicin Masarauta: Kwankwaso Ya Bayyana Masu Son Kawo Hargitsi a Kano

  • Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi zargin cewa wasu maƙiyan jihar Kano na ƙoƙarin kawo hargitsi a jihar kan rikicin masarauta
  • Jagoran na jam'iyyar NNNP ya yi kira ga al'ummar jihar da su haɗa kai domin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar
  • Tsohon gwamnan na jihar Kano ya bayyana cewa maƙiyan jihar sun mayar da batun masarautar siyasa domin adawa da rushe sababbin masarautun da aka yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Jagoran jam'iyyar NNPP na ƙasa kuma madugun Kwankwasiyya, Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi zargin cewa maƙiya Kano na shirin ruguza jihar.

Rabiu Kwankwaso wanda a baya ya taɓa zama gwamnan Kano, ya yi kira ga al’ummar jihar da su haɗa ƙarfi da ƙarfe domin samar da zaman lafiya da cigaba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bankaɗo abin da ya faru a 2019, ya tona masu rura wutar rikicin sarauta

Kwankwaso ya yi magana kan rikicin sarautar Kano
Kwankwaso ya zargi makiya Kano da kokarin kawo hargitsi Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Kwankwaso ya yi kira ga mutanen Kano

Kwankwaso ya yi wannan kiran ne a wajen bikin Sallah na musamman da gidauniyar Kwankwasiyya Development Foundation ta shirya a Kano, wanda aka gudanar a gidansa jiya Talata, cewar rahoton jaridar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce lokaci yayi da duk ƴan asalin Kano da ƴan jam’iyyar NNPP za su haɗa kai, bisa la’akari da matsalolin da jihar ke fuskanta daga manyan ƴan siyasa daga ɓangarori daban-daban, rahoton Voice of Nigeria ya tabbatar.

Fadar shugaban ƙasa ta musanta zargin da Kwankwaso ya yi cewa gwamnatin tarayya na shirin sanya da dokar ta ɓaci a Kano kan rikicin masarautar da ake yi.

Me Kwankwaso ya ce kan rikicin sarauta?

Dangane da rikicin masarautar Kano, Kwankwaso ya ce maƙiyan jihar sun mayar da abin siyasa domin adawa da dawo da ainihin yadda gidan sarautar yake a baya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya shiga babbar matsala, jam'iyyar APC ta nemi jami'an tsaro su kama shi

"Mun lashe zaɓe da gagarumin rinjaye amma maƙiyan jihar na ƙoƙarin ƙwacewa, amma Allah cikin ikonsa bai bar su ba."
"Alamu sun nuna kamar maƙiyan sun ƙara dawowa. Kun san abin da ke faruwa dangane da masarauta sannan muna godiya ga dukkanin masu goyon bayan gwamnati."

- Rabiu Musa Kwankwaso

APC ta buƙaci a cafke Kwankwaso

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam’iyyar APC reshen jihar Kano, ta yi kira ga hukumomin tsaro da su gaggauta cafke Rabiu Kwankwaso, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP.

Hakan na zuwa ne bayan Kwankwaso ya zargi gwamnatin tarayya ƙarƙashin jam’iyyar APC da ƙyanƙyasar sababbin ƴan ta’adda a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng