Kotu Ta Yi Hukunci Kan Bukatar Abba Kyari Ta Neman Sabon Beli

Kotu Ta Yi Hukunci Kan Bukatar Abba Kyari Ta Neman Sabon Beli

  • Babbar kotun tarayya da ke zamanta a birnin tarayya Abuja ta yi watsi da buƙatar sake neman sabon beli da Abba Kyari ya yi a gabanta
  • Alƙalin kotun wanda ya yanke hukuncin ya bayyana cewa buƙatar neman belin da dakataccen mataimakin kwamishinan ƴan sandan ya yi ba ta cancanta ba
  • Mai shari'a Emeka Nwite wanda ya yanke hukuncin ya nuna cewa Abba Kyari bai kawo hujjar da za ta sanya a amince da buƙatarsa ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar neman sabon belin da DCP Abba Kyari ya yi a gabanta.

Abba Kyari wanda yake fuskantar tuhumar safarar miyagun ƙwayoyi ya buƙaci a ba da belinsa har zuwa lokacin da za a kammala shari'arsa.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya bankaɗo abin da ya faru a 2019, ya tona masu rura wutar rikicin sarauta

Kotu ta ki ba da belin Abba Kyari
Kotu ta yi watsi da bukatar Abba Kyari ta neman sabon beli Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

A hukuncin da kotun ta yi wanda mai shari'a Emeka Nwite ya yanke a ranar Laraba, ya ce buƙatar DCP Abba Kyari ba ta cancanta ba, cewar rahoton jaridar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa kotu ta hana Abba Kyari beli?

Alƙalin kotun ya bayyana cewa dakataccen kwamishinan ƴan sandan bai kawo wani ƙwaƙƙwaran dalilin da zai sanya a ba da belinsa ba, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.

Mai shari'a Nwite ya nuna cewa kotun ko a baya ta taɓa watsi da irin wannan buƙatar belin da ya nema tare da ba da umarnin a gaggauta sauraron ƙarar.

Ya bayyana cewa ba a kawo wata hujja wacce za ta sanya kotun ta sauya matsaya kan hukuncin da ta yi a baya ba.

A bisa hakan, sai kotun ta ƙi amincewa da ba da belin sannan ta ba hukumar NDLEA damar ci gaba da tuhumar Abba Kyari da sauran waɗanda ake ƙara a shari'ar.

Kara karanta wannan

Sallah: Buhari ya fadi abin da 'yan Najeriya suka yi da ya faranta masa rai

Hukuncin na zuwa ne kusan wata ɗaya bayan kotun ta saki Abba Kyari na wucin gadi daga gidan gyaran hali domin ya je jana'izar mahaifiyarsa.

An taba ba da belin Abba Kyari

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban kotun tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba da belin dakataccen mataimakin kwamishinan ƴan sanda, DCP, Abba Kyari.

Mai shari'a Kolawole Omotosho ne ya ba da balin ɗan sandan mai fuskantar tuhuma kan safarar miyagun ƙwayoyi bayan ya shafe watanni a tsare a gidan gyaran hali.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng