Manyan Labarai A Yau
Ofishin jakadancin Amurka ya aika da sakon gargadi na tsaro kan Amurkawa da ke zaune a Najeriya. An gargade su da su guji yin tafiye-tafiye zuwa wasu wurare a Abuja.
Bayan hallaka 'yan daurin aure a Filato, an yi wa 'ya 'yan Sheikh Ibrahim Khalil kisan gilla. Gwamna ya yi Allah-wadai da kisan matasan, ya kira shi rashin imani/
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya nuna shakku kan cewa da wuya hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta yi rajistar sabuwar jam'iyya.
Farfesa Nasir Hassan-Wagini na jami'ar UMYU da ya ke sayar da kayan miya, ya shawarci matasa da dalibai da su rungumi sana'o'in hannu maimakon zaman banza.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani ya aika sako ga takwarorinsa na sauran jihohi. Ya bukaci gwamnonin da su kare 'yancin da 'yan kasa suke da shi na zirga-zirga.
Jami'an hukumar tsaron farin kaya (DSS) da wasu sauran hukumomin tsaro sun cafke wasu da ake zargin 'yan bindiga ne bayan sun daw daga aikin Hajji a Saudiyya.
'Yan daba sun farmaki hedkwatar jam'iyyar SDP ta kasa a ranar Talata. 'Yan daban sun farmaki hedkwatar am'iyyar ne biyo bayan dakatar da shugaban jam'iyyar.
Hukumar FDA ta amince da lenacapavir, matsayin rigakafin HIV. Amma UNAIDS ta bukaci a rage farashinsa da ya kai $28,218 don ya isa ga duniya baki ɗaya.
Kasar Isra'ila ta ce za ta cigaba da kai hare hare zuwa Iran bayan cimma yarjejeniya a tsakaninsu. Isra'ila ta ce Iran ta karya yarjejeniya amma ta musa.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari