Manyan Labarai A Yau
Gwamnatin jihar Sokoto ta gindaya sharadi kafin yin zaman sulhu da Bello Turji. Ta bukaci dan bindigan da ya sako mutanen da ya sace tare da daina kai hare-hare.
Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin, ya rasu yana da shekaru 90 a duniya bayan mulkinsa na shekara guda, ya bar gadon zaman lafiya da ci gaba a Ibadan.
An yi babban rashi a jihar Oyo bayan rasuwar daya daga cikin manyan sarakunan da ake ji da su. Olubadan na Ibadan, Oba Owolabi Olakulehin ya rasu.
Wannan rahoto ya duba muhimman gudunmawar da za a ci gaba da tunawa da su a game da Dantata — daga ilimi da lafiya zuwa taimakon gaggawa, addini da ci gaban al’umma
Gwamna Abba Yusuf ya naɗa ƙarin manyan masu taimaka masa na musamman guda 19 don ƙarfafa shugabanci tare da fatan za su ba da gudunmawa ga ci gaban Kano.
Fulani a Bauchi sun ƙi amincewa da sababbin masarautun da Gwamna Bala Mohammed yake son kirkirowa, sun ce sun fi son bin tsofaffin masarautun jihar 6.
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana cewa idan ya samu damar zama shugaban ƙasa a 2027, zai yi sheksra huɗu ne kaɗai don mutunta tsarin karɓa karɓa.
Sabon rikici ya ɓarke a Lamurde da Guyuk a jihar Adamawa, inda gidaje biyu suka ƙone, rundunar ‘yan sanda ta fara bincike tare da tura jami’an tsaro yankin.
Mai martaba sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II ya bayyana cewa ya zama dole lauyoyi su koyi amfani da fasahar zamani idan suka son aikinsu ya tsira.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari