Manyan Labarai A Yau
Rahotanni da muke samu yanzu na nuni da cewa Allah ya karbi rayuwar fitaccen ɗan kasuwar Kano da Arewa, Alhaji Aminu Ɗantata. Ya rasu yana da shekaru 94.
Rahotanni sun nuna cewa an matsar da jana'izar marigayi Alhaji Aminu Ɗantata daga lokacin sallar la'asar zuwa bayan Magriba a masallacin Annabi SAW da ke Madina.
An kashe mutum 1 bayan rikici kan gado ya barke tsakanin 'yan uwa; Shugaban Mikang ya yi Allah-wadai da rikicin, ya roƙi iyalan wanda aka kashe da kada su dau fansa.
Gwamna Abdulrazaq na jihar Kwara ya maka tsohon ɗan Majalisar tarayya, Moshood Mustapha, da ɗan'uwansa a kotu kan zargin wallafa bidiyon da zai tunzura jama'a.
Gwamnatin Najeriya ta tabbatar da cewa an ɗage jana'izar marigayi Alhaji AminuƊantata zuwa gobe Talata a birnin Madina saboda cika sharuɗdan Saudiyya.
Hukumomin Saudiyya sun amince a binne Alhaji Aminu Dantata a Madina ranar Litinin, bayan rasuwarsa yana da shekaru 94, an yi masa jana'izar Ga'ib a Kano.
Wani ɗan ƙasar Isra'ila, Avi Warshaviak, ya rasu bayan ya yanke jiki ya fadi a Otel ɗin Corinthia Villa da ke Garki a Abuja. An tuntubi ofishin jakadancin Isra'ila.
Babban mai ba da shawara kan harkokin yada labarai ga mukaddashin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Umar Iliya Damagum, ya yi murabus daga kan mukaminsa.
Wani bam da ake zargin 'yan ta'adda ne suka dasa shi ya yi sanadiyyar rasuwar mutane a jihar Yobe. Wasu mutane kuma sun jikkata sakamakon fashewar.
Manyan Labarai A Yau
Samu kari