Labarin Sojojin Najeriya
Rundunar sojojin Najeriya ta sanar da cewa ta kammala binciken kan harin bam wanda ya hallaka masu gudanar da Mauludi a kauyen Tudun Biri na jihar Kaduna.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar yin galaba kan 'yan ta'adda a jihohin Katsina da Plateau. Sojojin sun sheke dan ta'adda tare da ceto mutum biyu.
Sojojin Najeriya sun yi nasara kan 'yan ta'adda a jihohin Taraba da Filato tare da kwato makamai. Rundunar sojin ta sanar da nasarar ne a jiya Talata
Rundunar sojojin saman Najeriya ta kai hare-hare kan maboyar 'yan ta'addan da suka addabi mutane a jihar Neja. An hallaka tsagerun tare da lalata maboyarsu.
Hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya kawo mafita kan yadda za a dakile matsalar tsaron kasar inda ya ce hadin kai ne kadai zai kawo karshenta.
Gwannatin jihar Katsina ta yi alhinin kisan da 'yan bindiga suka yi wa wani kwamandan sojoji a jihar. Ta bayyana cewa kisan da aka yi masa babban rashi ne ga jihar.
Hedkwatar tsaron Najeriya ta ce sojoji ba za su yi ƙasa a guiwa ba har sai sun ga bayan duk wani nau'in ta'addanci a faɗin ƙasar nan domin zaman lafiya ya samu.
Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun samu nasarar hallaka wasu 'yan ta'adda guda bakwai a yayin wani artabu da suka yi a jihar Sokoto. Sun kwato makamai.
Sarkin Kwatarkwashi a jihar Zamfara, Abubakar Ahmed Umar ya bayyana cewa 'yan ƙasashen ketare da kuma ma'adinai a Arewacin Najeriya ne silar matsaar tsaro.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari