Sojojin Juyin Mulkin Nijar Sun Soke Bizar Jakadan Faransa, Sun Ba 'Yan Sanda Umarnin Fitar Da Shi Waje

Sojojin Juyin Mulkin Nijar Sun Soke Bizar Jakadan Faransa, Sun Ba 'Yan Sanda Umarnin Fitar Da Shi Waje

  • Sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijar sun sanar da wani sabon mataki mai tsauri a kan ƙasar Faransa
  • Sun soke biza da sauran takardun diflomasiyya na jakadan ƙasar Faransa da iyalansa da ke Nijar
  • Sun ce yanzu ba shi da wata rigar kariya da yake samu a baya, sun kuma umarci 'yan sanda su fitar da shi

Niamey, jamhuriyar Nijar - Sojojin juyin mulkin Nijar sun sanar da cewa daga ranar Alhamis, 31 ga watan Agusta, sun soke duk takardun diflomasiyya na jakadan Faransa a ƙasar wato Sylvain Itte.

Haka nan sojojin sun soki bizarsa da ta iyalansa tare da bai wa jami'an 'yan sanda umarnin su fitar da shi daga ƙasar kamar yadda Africa News ta ruwaito.

Sojojin Nijar sun umarci 'yan sanda su yi waje da jakadan Faransa
Sojojin juyin mulkin Nijar sun umarci 'yan sandan kasar da su fitar da jakadan Faransa daga ƙasar. Hoto: @jcokechukwu
Asali: Twitter

Me ya sa aka kori jakadan Faransa daga Nijar

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Faɗawa ECOWAS Da AU Abinda Ya Kamata Su Yi Dangane Da Juyin Mulki

A makon da ya gabata ne dai sojojin da suka yi juyin mulkin Nijar, suka bai wa jakadan ƙasar ta Faransa sa'o'i 48 ya fice daga ƙasar saboda zarginta da yin abubuwan da suke cutar da 'yan Nijar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Haka nan ma ana ganin ƙin amsa gayyatar ganawa da sabon Firaministan jamhuriyar Nijar da ofishin jakandancin ya ƙi yi, ya ƙara janyo fushin sojojin a kansu.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya yi wani rahoto, inda shugaban Faransa Emmanuel Macron ya jaddada cewa jakadan ba zai bar Nijar ba, kuma har yanzu suna goyon bayan hamɓararren shugaban ƙasa Mohamed Bazoum.

Sojojin Nijar sun ce ba za su maida Bazoum kan kujerarsa ba

A wani rahoto na daban da Legit.ng ta kawo mu ku a baya, kun ji yadda tattaunawa ta kasance tsakanin Janar Abdulsalami Abubakar da shugabannin juyin mulkin Nijar kan batun dawo da Bazoum.

Kara karanta wannan

Sojojin Juyin Mulkin Gabon Sun Zayyano Dalilai 4 Da Suka Sanyasu Kifar Da Gwamnatin Kasar

Sojojin sun shaidawa Abdulsalami cewa batun dawo da Bazoum kan kujerarsa ba mai yiwuwa ba ne tunda sun riga da sun kifar da shi.

Sai dai sun ce a shirye suke su yi kowace irin tattaunawa ce ake buƙatar a yi da su, amma banda batun dawo da mulki ga Bazoum.

Atiku ya shawarci ECOWAS da AU kan juyin mulki

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan martanin ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar dangane da juyin mulkin da aka yi a ƙasar Gabon.

Atiku ya yi Allah wadai da abinda ya faru sannan kuma ya shawarci ECOWAS da AU da su zauna da sojojin juyin mulkin Nijar domin ganin sun ajiye mulki sun koma barikokinsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel