Juyin Mulkin Gabon: Sojoji Sun Zayyano Dalilai 4 Da suka Sanya Su Kwace Mulki Hannun Shugaba Ali Bongo

Juyin Mulkin Gabon: Sojoji Sun Zayyano Dalilai 4 Da suka Sanya Su Kwace Mulki Hannun Shugaba Ali Bongo

  • Ainihin dalilan da suka sa aka hamɓarar da gwamnatin Ali Ondimba Bongo sun bayyana
  • An lissafo siyasa, tattalin arziƙi da kuma walwalar jama'a a cikin dalilan da suka janyo juyin mulkin
  • Sojojin sun kuma bayyana cewa zaɓen ƙasa da aka kammala a ranar Asabar ɗin da ta gabata ba ya da sahihanci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gabon, Libreville - Hafsoshin sojojin kasar Gabon, ƙarƙashin kwamitin miƙa mulki da maido da hukumomi (CTRI), sun bayyana dalilan da suka sa aka hamɓarar da Shugaba Ali Ondimba Bango daga kan karagar mulki.

Rundunar soji ta sanar a gidan talabijin na kasar cewa, yanzu sojoji ne ke riƙe da madafun iko bayan karɓe mulki daga Bongo, a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta.

Sojojin Gabon sun fadi dalilin kifar da gwamnatin Ali Bongo
Sojojin Gabon sun fadi manyan dalilai 4 da suka sanyasu yin juyin mulki. Hoto: The Pledge
Asali: UGC

Me yasa sojojin Gabon suka hamɓarar da Ali Bongo

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sojoji Sun Sake Hambarar Da Gwamnatin Farar Hula a Nahiyar Afirika

Kamar yadda tashar talabijin ta France24 ta wallafa, sojojin sun bayyana dalilan da suka sanyasu aiwatar da juyin mulkin kamar haka:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Siyasa, tattalin arziƙi da rikicewar al'amurra

Sojojin sun koka cewa a can baya abubuwa na tafiya yadda ya kamata saɓanin yadda komai yake tafiya a yanzu.

Sun bayyana cewa cewa yanzu haka ana fama da rikice-rikece a ɓanagaren hukomi, siyasa, tattalin arziƙi da kuma ɓangaren walwalar al'umma.

2. Zaben da aka gudanar ba ya da sahihanci

Sojojin sun kuma bayyana cewa, zaɓen shugaban ƙasar da aka kammala a ranar Asabar ɗin ta gabata, ba ya da sahihanci, cike yake da maguɗi.

Sun ce yadda aka gudanar da zaɓen bai yi daidai da abinda ɗaukacin 'yan ƙasar ta Gabon ke so ba.

3. Taɓarɓarewar al'amura

Sojojin juyin mulkin na ƙasar Gabon sun kuma bayyana cewa daga cikin dalilansu na aiwatar da juyin mulki akwai taɓarɓarewa al'amura.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Zai Biya Mazauna Abuja Diyyar N825m,.Ya Bayyana Dalili

Sun ce abubuwa ba sa tafiya a daidai, wanda hakan ke neman jefa ƙasar cikin mummunan yanayi.

4. Gudun faɗawar ƙasar cikin rikici

A yayin da suke sanar da batun juyin mulkin a ranar Laraba, 30 ga watan Agustan shekarar 2023, sojojin sun ce sun hamɓarar da gwamnati mai ci ne saboda su kare ƙasar daga faɗawa cikin rikici.

Sun kuma ba da sanarwar soke zaɓen ƙasar da ya kammala ranar Asabar, da kuma sanar da rufe iyakokin ƙasar kamar yadda The Africa Report ta kawo.

Wannan juyin mulki na Gabon na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar ECOWAS ke ci gaba da ƙoƙarin dawo da dimokuraɗiyya a jamhuriyar Nijar biyo bayan juyin mulki.

Jigon APC ya yi martani kan juyin mulkin ƙasar Gabon

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan martanin da jigo a jam'iyyar APC, Femi Fani-Kayode ya yi dangane da juyin mulkin da aka yi a ƙasar Gabon.

Kara karanta wannan

Miyagun 'Yan Daba Da Haɗin Kan 'Yan Sanda Sun Kai Kazamin Hari Sakatariyar Jam'iyya, Sun Yi Ɓarna

Fani-Kayode ya bayyana cewa wannan wani abu ne da ya hango faruwarsa a wasu daga cikin ƙasashen Afrika ta Yamma da kuma Afrika ta Tsakiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel