Labaran garkuwa da mutane
Yan bindigar sun nemi iyalan su tara masu kudin fansa naira miliyan 10 da buhunan shinkafa uku, nan da sati daya ko kuma su zama silar asarar rayukan ‘yan uwansu.
Tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da fasinjoji 13 daga kamfanin sufuri mallakin Gwamnatin jihar Bunue ranar 9 ga watan Nuwamba, 2023 a titin Naka-Makurdi.
Wasu miyagun yan bindiga sun yi garkuwa da shugaba ƙaramar hukuma mace da aka dakatar, Amina Audu, tare da direbanta ranar Litinin, 13 ga watan Nuwamba da safe.
Idan manomi ya yi sa'a gonarsa ta yi kyau, sai ya biya kusan N100, 000 kafin ya yi girbi. ‘Yan bindiga na karba a hannun manoma kafin a cire kayan gona a Kaduna.
Yan bindiga sun kai hari yankin Gandu da ke kusa da jami'ar tarayya da ke Lafiya a jihar Nasarawa, sun harbi ɗalibi ɗaya sun tafi da wani ɗan kasuwa zuwa cikin daji.
Tsagerun 'yan bindiga sun yi garkuwa da mutum uku ciki harda ƴan uwan juna a garin Bmuko, ƙaramar hukumr Bwari da ke birnin tarayya Abuja, sun nemi fansa.
Dakarun sojoji da haɗin guiwar ƴan sanda sun samu nasarar ceto ƴan bautar ƙasa biyu duk mata daga hannun 'yan bindiga a jihar Katsina ranar Alhamis.
Tsageru ɗauke.da muggan makamai sun kai farmaki har cikin gida, sun yi awon gaba da shugaban ma'aikatan shugaban majalisar dokokin jihar Adamawa.
Gwamnan jihar Abia, Alex Otti, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta kai samame kusa da kasuwar shanu, ta tsinci gawarwakin mutane sama da 70 a yanayi mara daɗi.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari