Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Musulunci, Matarsa Da Yara 2 a Kaduna

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Musulunci, Matarsa Da Yara 2 a Kaduna

  • Yan bindiga sun sace wani babban malamin musulunci, matarsa da kuma 'ya'yansa biyu a jihar Kaduna
  • Daga cikin yaran malamin da aka sace harda jariri mai kwana daya kacal a duniya
  • Maharan da suka sace Malam Abubakar Mushawy Ibrahim da iyalinsa sun nemi a biya naira miliyan 20 kudin fansa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kaduna - Wasu da ake zaton yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani malamin addinin Musulunci, Malam Abubakar Mushawy Ibrahim, tare da matarsa da yaransu biyu a jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa daya dana cikin yaran ya kasance jariri dan kwana daya lokacin da aka yi garkuwa da su a ranar Laraba da ta gabata.

An sace malami da iyalinsa a Kaduna
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Malamin Musulunci, Matarsa Da Yara 2 a Kaduna Jami'an yan sanda Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Yan bindigar sun shiga gidan malamin da ke Fondisho, wani gari a hanyar babban titin Kaduna zuwa Zariya.

Kara karanta wannan

Kisan Albanin Kuri: Iyalan Malamin Da Aka Kashe Sun Bayyana Halin Da Suke Ciki, Sun Ba Da Sako Ga Gwamnati

Yan bindiga sun yi garkuwa da malami da iyalinsa mai jego, majiya

A cewar wasu majiyoyi a yankin, an yi garkuwa da mutanen ne kwana daya bayan matar malamin ta haihu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yan bindigar na neman miliyan 20 kudin fansa

Wani makusancin malamin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya bayyana cewa malamin shine shugaban makarantar Hayatul Islamiyya Kawo, jihar Kaduna.

"Shi da matarsa da ta haifi sabon jinjiri, da dayan dansa aka sace gaba daya. Yanzu haka ba a san inda suke ba su dukka hudun. Abun takaici, yan bindigar na neman a biya kudin fansa naira miliyan 20," inji majiyar.

Majiyar ta koka cewa yan uwan mutanen da abun ya ritsa da su talakawa ne kuma sun gaza hada kudin fansar.

Jaridar Aminiya ta kuma rahoto cewa mukaddashin kakakin yan sandan jihar, Mansur Hassan, ya yi alkawarin tuntubar ta bayan ya samu cikakken bayani daga wajen DPO na yankin amma har yanzu ba a ji daga gare shi ba.

Kara karanta wannan

Wani Dan Fashi Da Makami Da Aka Kama Ya Ambaci Sunan Sifetan 'Yan Sandan Da Ke Basu Bindigu

Yan bindiga sun yi garkuwa da basaraken arewa da matarsa

A wani labari makamancin wannan, mun ji a baya cewa tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da basaraken garin Gurku da ke karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, Jibril Mamman Waziri, da matarsa, Hajiya Sa’adatu Waziri.

An rahoto cewa al'amarin ya afku ne da misalin karfe 10 na dare lokacin da mazauna yankin da dama suka kwanta bacci domin samun hutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel