Labaran garkuwa da mutane
Masu garkuwa da mutane sun sako amarya mai suna Rukkayat Musa da ƙannen mijinta mata guda biyu da suka sace a jihar Kwara. An biya N7m a matsayin kuɗin fansa.
DSS ta ankarar da al’umma cewa akwai shirye-shirye aukawa wuraren bauta da filayen wasanni. Dr. Peter Afunanya ya ce DSS da Sojoji da ‘Yan Sanda sun gano hakan.
Wasu tsagerun 'yan bindigan daji sun sheƙe manoma uku, sun tattara wasu manoman da matafiya da ke kan hanyar zuwa kasuwa a Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
'Yan bindiga sun sace wata manajar bankin Sterling Mai suna Nneka Unoka a jihar Bayelsa yayin da take kan hanyarta na zuwa wurin aiki a cikin birnin Yenagoa.
Yan bindiga sun yi garkuwa da basarake Shedrack Durojaiye Obibeni, da mai ɗakinsa a ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas da ke jihar Kogi, da yammacin ranar Litinin.
Wasu yan bindiga da ba'a san ko su waye ba sun halaka ma'aikacin hukumar zabe INEC, Emmanuel Igwe, a jihar Ebonyi yayin da yake hanyar dawowa daga jihar Abiya.
Miyagun sun je gidan Basarake sun bindige shi, sun bi daki-daki, sun kashe ‘ya‘yansa. Ardon birnin Zazzau da kewaye ya na barzahu a dalilin ta’adin ‘yan bindiga
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda zai tura kudiri zuwa majalisa domin inganta tsaro. Tuni mutane su ka fara yabawa wannan mataki da sabon Gwamna ya dauka
Tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da da babban limamin masallacin Uso da ke karamar hukumar Akure ta arewa a jihar Ondo, Alhaji Ibrahim Bodunde Oyinlade.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari