Yan Bindiga Sun Sace Kwararren Likita a Bakin Aiki a Jihar Benuwai

Yan Bindiga Sun Sace Kwararren Likita a Bakin Aiki a Jihar Benuwai

  • 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wani kwararren Likita da wata mata da ba a gano ko wacece ba a jihar Benuwai
  • Rahoto ya nuna cewa Likitan na kan hanya zai je aiki lokacin da maharan suka tare shi a yankin ƙaramar hukumar Ukum
  • Hukumar yan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce dakarunta sun fara bincike da nufin ceto likitan

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Benue State - Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da wani kwararren likita mai suna Dr. Msuega Asema a unguwar Ugbaam, gundumar Biam a karamar hukumar Ukum a jihar Benuwai.

Shaidu sun ce, an yi garkuwa da Dakta Asema, wanda ke aiki a babban asibitin Sankera a cikin garin ZakiBiam ranar Lahadi da misalin karfe 1:00 na rana yayin da yake bakin aiki.

Yan bindiga sun sace Likita a Benuwai.
Yan Bindiga Sun Sace Kwararren Likita a Bakin Aiki a Jihar Benuwai Hoto: vanguardngr
Asali: Twitter

Mazauna yankin sun ce an sace likitan ne tare da wata mata da ba a tantance wacece ita ba har kawo yanzu, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: An Ƙara Samun Fashewa a Najeriya, Mutane Sama da 20 Sun Mutu

An ce Likitan ya shiga hannun maharan ne yayin da yake kan hanyarsa ta sa ido kan shirin yaki da cutar zazzabin cizon sauro na Jiha (SMC) da ke gudana a shirin Tallafin Iyali (FSP), Uyoo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wakilin jaridar Vanguard ya gano cewa tuni marasa lafiya sun taru suna jiran likitan a Asibiti, inda yake zuwa ya duba su.

Amma daga bisani aka sanar da mutanen da suka taru cewa yan bindiga sun yi awon gaba da Likitan a hanyarsa ta zuwa Asibitin garinsu kamar yadda ya saba.

Mazauna yankin sun ƙara da bayanin cewa sun kira Likitan ta wayar salula kuma ya faɗa musu cewa bai san a inda yake ba, sannan maharan sun ɗaure masa ido da kyalle.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Jami'ar hulɗa da jama'a ta rundunar 'yan sanda reshen jihar Benuwai, SP. Catherine Anene, ta tabbatar da aukuwar lamarin.

Kara karanta wannan

A Kurarren Lokaci, Tinubu Ya Cire Mutum 4 a Jerin Wadanda Za A Ba Kujerar Minista

Kakakin rundunar yan sandan ta bayyana cewa a halin da ake ciki yanzu jami'ai na kan bincike don kubutar da likitan.

Yan Sanda Sun Kama Sama da Mutum 100 da Ake Zargi da Aikata Laifuka a Bauchi

A wani rahoton kuma Jami'an yan sandan jihar Bauchi sun samu nasarar damƙe waɗanda ake zargi da aikata muggan laifuka sama da 100 cikin wata guda.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi , Mista Auwal Muhammad, shi ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel