Bokan Da Masu Garkuwa Suka Sace Ya Ce Gudun Asarar Rayukan Jama'a Yasa Ya Yarda Aka Tafi Da Shi

Bokan Da Masu Garkuwa Suka Sace Ya Ce Gudun Asarar Rayukan Jama'a Yasa Ya Yarda Aka Tafi Da Shi

  • Shahararren boka da masu garkuwa da mutane suka sace ya shaƙi iskar 'yanci bayan shafe kwanaki hannunsu
  • Ya ce abokansa ne suka kira shi zuwa otal ɗinsa domin nema musu sauƙi kan kuɗaɗen da suka kashe
  • Ya ce ya zaɓi ya bi masu garkuwa da mutanen ne domin gudun samun asarar rayukan mutanen da ke farfajiyar otal ɗin

Anambra - Shahararren boka ɗan jihar Anambra, Akwa Okuko Tiwara Aki, wanda aka fi sani da Oba, ya yi bayani bayan kuɓutarsa daga hannun masu garkuwa da mutane.

Ya ce ya haƙura da ɓacewa ne don gudun asarar rayukan jama'a a lokacin da aka zo tafiya da shi kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

Labarin satar bokan da masu garkuwa da mutane suka yi, a lokacin da yake shan shagalinsa tare da abokansa, ta karaɗe kafafen sada zumunta a cikin 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Dalilin Da Ya Sanya 'Yan Bindiga Suka Kwamushe Ni, Babban Boka Ya Yi Bayani Bayan Ya Shaki Iskar 'Yanci

Bokan da masu garkuwa da mutane suka sace a Anambra ya yi jawabi bayan kubutarsa
Bokan da masu garkuwa da mutane suka sace a Anambra ya bayyana abinda ya hana shi ɓacewa lokacin da za a tafi da shi. Hoto: Monachiso Madueke Hot 5
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abokansa ne suka kira shi zuwa otal ɗinsa

Masu garkuwa da mutanen sun sako bokan a ranar Asabar, bayan shafe kwanaki a hannunsu.

Bokan ya bayyana cewa a ranar da abin ya faru, abokansa ne suka kira shi a wata, inda suka shaida masa cewa suna otal ɗinsa kuma sun kashe kuɗaɗe da yawa.

Ya ce abokan sun buƙaci ya zo domin su samu sauƙi kan sama da naira 300,000 da suka kashe a otal ɗin nasa.

Harsashin bindigar masu garkuwar bai yi tasiri a kansa ba

Akwa ya bayyana cewa ya bar gidansa domin zuwa ya haɗu da abokan nasa dake jiransa a Otal.

Ya ce da isarsa ne masu garkuwar suka fara harbi ta ko ina, inda a cikin hakan ne suka buɗe masa wuta, wanda ya ce hakan bai tasiri a kansa ba.

Kara karanta wannan

Dara Ta Ci Gida: 'Yan Bindiga Sun Sace Babban Boka Mai Bayar Da Maganin Bindiga Cikin Tsakar Dare

Sai dai ya ce 'yan bindigar sun halaka masu tsaron lafiyarsa biyu, inda daga nan ne suka tura shi cikin motarsu kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Akwa ya ƙara da cewa ya aminta da ya bisu ne maimakon ya yi kayar zana, domin gudun kar a cutar da ƙarin wasu mutanen da ke a farfajiyar otal ɗin.

An gurfanar da boka gaban kotu bisa zargin sace motar Fati Muhammad

Legit.ng a baya ta kawo labarin gurfanar da wani boka a gaban wata kotun shari'ar Muslunci da ke Kano da aka yi, bisa zargin sace motar jaruma Muhammad.

Bayanai sun nuna cewa bokan ya haɗa baki ne da wani ɗan uwanta, inda suka ɗura ma ta wani rubutu da ya gusar da hankalinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel