Labaran garkuwa da mutane
Dan majalisar Zurmi da Shinkafa ya bayyana cewa al'ummar kauyuka 50 a yankin Zurmi sun gudu sun bar gidajensu saboda yawan hare-haren ƴan bindiga a kwanan nan.
Rundunar yan sanda a jihar Delta ta tabbatar da kama masu garkuwa da mutane da dama dauke da makamai tare da wani matsafi dauke da gashin dan Adam.
An kama wasu matasa a jihar Neja bisa zargin sace fankoki a masallaci, inda aka kama wani kuma da laifin datse hannun wani dan acaba da kuma sace babur.
Tsagerun ƴan bindiga sun kai hari kauyen Bilbis, sun kashe mazauna garin da dama da suka haɗa da maza, mata da kananan yara, sn yi masu jana'iza yau Jumu'a.
Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya ce tuni jami'an tsaro da mafarauta suka kaewaye daji da yankin jami'ar da ƴam bindiga suka kai hari jiya.
Majalisar wakilan Najeriya nan ta bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dauko hayar sojojin haya daga kasashen waje domin magance rashin tsari a kasar nan.
Majalisar wakilan tarayya ta ɗauki wasu matakai da nufin magance yawaitar garkuwa da ɗalibai a makarantun ƙasar nan da kuma dawo da tsaro a faɗin Najeriya.
Yan sandan jihar Ogun sun sanar da kashe masu garkuwa da mutane biyu tare da kwato kudin fansa naira miliyan 7.9. Sun kuma sanar da cewa suna kokarin kamo sauran.
Dakarun ƴan sanda sun cafke masu garkuwa da mutane yayin da barci ya kwasshe su bayan sun yi garkuwa da matar fasto da wasu mutum biyu a jihar Ondo.
Labaran garkuwa da mutane
Samu kari