Bayan an Kubutar da Dalibai 137, Gwamna Uba Sani Ya Fadi Hakikanin Adadin Yaran da Aka Sace

Bayan an Kubutar da Dalibai 137, Gwamna Uba Sani Ya Fadi Hakikanin Adadin Yaran da Aka Sace

  • Uba Sani ya bayyana adadin yawan daliban da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kuriga na ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna
  • Gwamnan ya tabbatar da cewa adadin ƴan makaranta 137 da aka ceto shi ne haƙiƙanin adadin yaran da aka tafi da su cikin daji
  • Sai dai, ya tabbatar da cewa malamin da aka sace tare da su, bai tsira ba bayan ya rasa ransa sakamakon rashin lafiya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana cewa ɗalibai 137 aka sace a Kuriga saɓanin 287 da ake ta yaɗawa.

An dai sace ɗaliban ne a ranar, 7 ga watan Maris, 2024, a ƙauyen Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun ta jihar.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan ceto daliban da aka sace a Kaduna, ya sha sabon alwashi

Uba Sani ya fadi yawan daliban da aka sace
Gwamna Uba Sani ya ce dalibai 137 aka sace sabanin 87 Hoto: Senator Uba Sani
Asali: Facebook

Ta wace hanya aka ceto ɗaliban Kuriga?

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels tv, a shirinsu na 'Sunday Politics' a ranar Lahadi, 24 ga watan Maris, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa sojoji ne suka ceto ɗaliban tare da haɗin gwiwar ƴan banga a jihar Zamfara.

Hedikwatar tsaro ta ƙasa, a ranar Lahadi ta ce an ceto jimillar ɗalibai 137, saɓanin rahotannin da ke cewa ƴan bindigan sun sace yara 287.

Uba Sani ya fadi adadi na gaskiya

Gwamnan ya ce adadin da sojoji suka fitar shi ne adadi na gaskiya, inda ya bayyana “287”, a matsayin wani tunani na wasu mutane.

A kalamansa:

"Ba na son na yi jayayya da kowa kan adadinsu. Abin da ya fi muhimmanci a wajena shi ne dawowar yaran cikin ƙoshin lafiya. Na yi murna sun dawo dawo lafiya, amma wannan adadin tunanin wasu mutane ne kawai.

Kara karanta wannan

Bayanai sun fito kan yadda aka ceto daliban da aka sace a jihar Kaduna

"Na gana da iyayen yaran sannan sun tabbatar mani da cewa adadin da sojoji suka bayar shi ne wanda yake daidai.

Gwamna Uba Sani, ya kuma bayyana cewa malamin da aka sace yaran tare da shi, ya rasa ransa a hannun ƴan bindigan sakamakon rashin lafiya.

Ceto dalibai: Tinubu ya yi tsokaci

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi maraba da kuɓutar da ɗaliban da aka sace a jihar Kaduna.

Shugaban ƙasan ya yi nuni da cewa ya kamata gwamnatocin jihohi su haɗa kai da gwamnatin tarayya, domin kaucewa sake aukuwar irin hakan a gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel