Gwamnatin Bola Tinubu Ta Faɗi Gaskiya Kan Biyan Kuɗin Fansa Yayin Ceto Ɗaliban Kaduna

Gwamnatin Bola Tinubu Ta Faɗi Gaskiya Kan Biyan Kuɗin Fansa Yayin Ceto Ɗaliban Kaduna

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa ko kwandala ba a biya da sunan kuɗin fansa ba yayin ceto ɗaliban makarantar Kuriga ta Kaduna
  • Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, Mohammed Idris, ne ya sanar da haka a fadar shugaban ƙasa bayan taron FEC ranar Litinin
  • Ya kuma miƙa sakon godiya ga NSA, hafsoshin tsaro da sauran waɗanda suka ba da gudummuwa wajen kuɓutar da yaran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Gwamnatin tarayya karƙashin shugaban kasa, Bola Tinubu, ta yi bayani kan raɗe-raɗin biyan kuɗinsa wajen ceto ɗaliban Kuriga a jihar Kaduna.

Gwamnati ta bayyana cewa ba a biya ko Naira ɗaya da sunan kuɗin fansar ɗaliban firmare da na sakandiren kauyen Kuriga da aka yi garkuwa da su ba.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta biya maƙudan kuɗin fansa wajen ceto ɗaliban Kaduna? Gwamna Sani ya faɗi gaskiya

Daliban Kuriga da Tinubu.
Gwamnatin Tarayya Ta Musanta Biyan Kuɗin Fansa Wurin Ceto Daliban Kaduna Hoto: Bayo Onanuga
Asali: Twitter

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, Mohammed Idris ne ya sanar da haka jim kaɗan bayan kammala taron majalisar zartarwa (FEC) a Abuja ranar Litinin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ne ya jagoranci taron FEC karo na 10 bayan kafa gwamnatinsa a fadar shugaban ƙasa yau Litinin, 25 ga watan Maris,2024.

A rahoton The Nation, ministan ya ce:

"Kamar dai yadda mai girma shugaban ƙasa ya yi alƙawari, an kuɓutar da su. Ko ƙwandala ba a biya a matsayin kuɗin fansa ba."

Tinubu ya godewa NSA

Idris ya kuma miƙa godiyar Tinubu ga mai ba da shawara kan tsaron kasa (NSA), manayan hafsoshin tsaro da sauran waɗanda suka taimaka wajen ceto ɗaliban.

Idan ba ku manta ba a kwanakin baya ne shugaba Tinubu ya sha alwashin cewa gwamnatin tarayya ba za ta biya kudin fansa ba domin a sako ɗaliban da aka sace.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi magana kan ceto daliban da aka sace a Kaduna, ya sha sabon alwashi

Ministan ya kara da cewa, shugaba Tinubu ya umurci jami’an tsaro da su kara kaimi wajen kawo karshen matsalar garkuwa da mutane a fadin kasar nan, rahoton Leadership.

"Shugaban kasa ya umarci jami’an tsaro da su tabbata sun kawo karshen garkuwa da mutane, kuma su zaƙulo duk wani mai hannu a laifin garkuwa da mutane domin a hukunta shi."

- Mohammed Idris.

Uba Sani ya yi magana kan kudin fansa

A wani rahoton kuma Gwamna Uba Sani ya ce kace-nace kan kuɗin fansar da aka biya wajen ceto ɗaliban Kuriga ba abu ne mai muhimmanci ba.

Ya bayyana cewa abu mafi muhimmanci shi ne gwamnati ta samu nasarar ceto dukkan ɗaliban da aka yi garkuwa da su cikin ƙoshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel