Jihar Kano
Wuta ta lakume ofisoshi da kayan aiki da gobara ta tashi a Hukumar shari’ar Kano. Tashin gobarar a ranar Talata ya tsayar da ayyukan Hukumar cak.
NNPP, APC sun sha bam-bam kan matsayin Abba da Gawuna da takardun kotu suka fito. Haruna Dederi ya yi ikirarin Abba yana nan a kujerar Gwamnan Kano.
Za a ji yadda takardun hukuncin kotu su ka birkita magoya baya tsakanin APC da NNPP a Kano. Takardun da aka fitar sun nuna Gwamna Abba Kabir Yusuf ya samu gaskiya.
Kotun ɗaukaka ƙara ta saki takardun hukuncin da ta yanke kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar Kano, wanda ya tsige Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP.
Tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo ya ce babu adalci alkalai guda uku ko hudu su sauya zabin miliyoyin mutane ba a zama daya na kotun zabe.
Ana bukatar takardun CTC domin jam’iyyar NNPP ta iya daukaka kara a shari’ar Kano. Takardun da ake bukata domin zuwa kotun koli ba su shigo hannun NNPP ba.
Wasu sun ce gaskiya kotu ba tayi adalci wajen zaftare kuri’u fiye da 165, 000 a zaben gwamnan Kano. Femi Falana SAN ya ce kotun koli za ta gyara wadannan kuskure.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya na ganin saboda Rabiu Musa Kwankwaso ake son raba shi da kujerar gwamna.Abba ya ce za su cigaba da aiki a karkashin jagorancin Kwankwaso.
Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano kuma jarumi a Kannywood, Abba El-mustapha ya sanar da rasuwar darakta, Aminu S Bono ranar Litinin.
Jihar Kano
Samu kari