Labari Kai Tsaye: Yadda Ake Yanke Hukuncin Zaben Gwamnan Jihar Kano a Kotun Koli

Labari Kai Tsaye: Yadda Ake Yanke Hukuncin Zaben Gwamnan Jihar Kano a Kotun Koli

Abuja - An yi zaben gwamnoni a jihohi kusan 30 a watan Maris a 2023, tun bayan lokacin ake shari’ar takarar a kotu.

A yau kotun koli za ta yanke hukunci a karshe a kan karar shari’ar wasu zaben da aka yi, daga ciki har da na Kano.

Kotun daukaka kara da kotun sauraron korafin zabe sun ba Nasiru Gawuna nasara, duk sun tige Abba Kabir Yusuf.

Abba ya ci zabe

Kotun koli ta tabbatar da nasarar NNPP a zaben gwamnan jihar Kano, ta karbi korafin Abba Kabir Yusuf.

Kotu ta dawo da kuri'un NNPP

Mai shari'a John Okoro ya ci gyaran kotunan baya, ya tabbatarwa Abba da NNPP kuri'u 165, 616 da aka soke a baya.

A game da batun zama 'dan jam'iyya, kotu ta ce ba ta da hurumin shiga sha'anin jam'iyya, tayi watsi da karar APC.

'Yan Kwankwasiyya a wajen kotu

Rahoton Daily Trust ya nuna magoya bayan Kwankwasiyya sun cika wajen kotun koli inda ake yanke hukunci a halin yanzu.

An zo kan shari'ar Kano

Kotun koli tayi hukunci a kan shari'o'in Legas da Bauchi, yanzu lokaci ya yi da za a saurari batun zaben gwamnan Kano.

Wole Olanipekun SAN yake kare Gwamna Abba Kabir Yusuf sai Nureni Jimmoh SAN yana mai kare jam’iyyar APC mai adawa.

John Okoro ya ce ana zargin Abba Kabir Yusuf da karyar zama ‘dan jam’iyya da kuma INEC da yin aringizon kuri’u a zaben 2023.

Alkalai sun iso kotu

Mai shari’a John Okoro ya jagoranci alkalai takwas cikin zauren kotun inda gwamnonin jihohi shida za su san matsayar kujerunsu.

Premium Times ta ce Mai shari’a Lawal Garba ya fara karanto shari’ar zaben gwamnan Legas, wanda da alama da shi za a fara yau.

Abba a Kotu

A wani bidiyo da aka wallafa a dandalin X, an ga isowar gwamnan kotu tare da mataimakinsa, Aminu Abdussalam

Darekta Janar na yada labarai a gidan gwamnatin Kano ya nuna hotunan Abba yana gaisawa da takwarorinsa a kotun.

Sanusi Bature Dawakin Tofa ya yi ikirarin wakilan NNPP ne kurum a kotu a lokacin yayin da ake jiran isowar alkalai.

Abba da Gwamnoni sun dura kotun koli

Rahoto daga jaridu sun zo cewa gwamnoni hudu sun dura kotun koli, inda ake jiran hukuncin manyan alkalan kasa.

Gwamnonin su ne: Bala Mohammed, Abba Yusuf, Caleb Mutfwang da Dauda Lawal na Bauchi, Kano, Filato da Zamfara.

Hadimin jagoran Kwankwasiyya, Saifullahi Hassan ya ce Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa sun isa kotun kolin.

Online view pixel