Jihar Imo
JIhohi biyar ne hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ta bayyana cewa sun fi kowace jiha a Najeriya sayen kayayyakin abinci da tsada. Cikin jihon akwai jihar Kwara.
Tsohon shugaban ma'aikatan jihar Imo, Uche Nwosu ya shawarci Bola Tinubu akan rabon kudaden tallafi inda ya ce ya kamata kudin su kai N30,000, don isa ga kowa.
Miyagun yan bindiga sun kai farmaki fadar basaraken Nguru, ƙaramar hukumar Aboh Mbaise a jihar Imo, sun kashe Sarki yayin da ya karɓi bakunci wani mutumi yau.
Yanzu muke samun labarin yadda gwamnan jihar Imo ya kara N10k kan albashin ma'aikatan jiharsa domin rage musu radadin abin da ke faruwa na tsadar man fetur.
Mataimakin kakakin majalisar wakilai ya bayyana cewa yankin Kudu maso Gabas ya yi asarar N4trn cikin shekara biyu a dalilin dokar zaman gida da IPOB ta kakaɓa.
Wata tsohuwa mai kimanin shekaru 74 a duniya ta bayyana yadda ta samu rauni na harbin bindiga yayin zabe don kare jam'iyyar Labour, amma babu wanda ya gaisheta.
Gwamnatin jihar Imo da ke shiyyar kudu maso gabashin Najeriya ta karyata jita-jutar cewa wasu miyagun yan bindiga sun kai farmaki sakatariyar jiha a Owerri.
Gwamna Hope Uzodimma na jihar Imo ya gana da takwaransa na jihar Lagas, Gwamna Babajide Sanwo-Olu kan rikicin Inyamurai yan kasuwa da Yarbawa a jihar Lagas.
Yayin da ake tunkarar zaben gwamnan jihar Imo a watan Nuwamba mai zuwa, gwamna Hope Uzodinma mai neman tazarce ya karɓi jiga-jigan PDP da suka sauya sheka.
Jihar Imo
Samu kari