Zaben Kogi, Imo da Bayelsa: Karuwar Rikici da Rashin Tsaro Abin Damuwa Ne, INEC

Zaben Kogi, Imo da Bayelsa: Karuwar Rikici da Rashin Tsaro Abin Damuwa Ne, INEC

  • Hukumar INEC ta ce yanayin tsaro da rikici tsakanin jam'iyyun siyasa babban abin damuwa ne a zaɓukan Imo, Kogi da Bayelsa
  • Kwamishinan yaɗa labaran INEC na ƙasa, Mista Sam Olumekun, ya ce zasu ci gaba da tuntubar masu ruwa da tsaki kan lamarin
  • INEC ta shirya gudanar da zaɓen gwamnoni a waɗan nan jihohi uku ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023

FCT Abuja - Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta nuna tsantsar damuwarta kan yanayin taɓarɓarewar tsaro da tada zaune tsaye a jihohin Imo, Bayelsa da Kogi.

Kamar yadda Daily Trust ta rahoto, INEC ta nuna damuwa kan abinda ke auku wa ne yayin da ake tunkarar zaben gwamnoni a jihohin guda uku ranar 11 ga watan Nuwamba.

Shugaban hukumar zaɓe INEC na ƙasa, Farfesa Mahmud Yakubu.
Zaben Kogi, Imo da Bayelsa: Karuwar Rikici da Rashin Tsaro Abin Damuwa Ne, INEC Hoto: INECNigeria
Asali: UGC

Daga cikin abin da INEC ke ganin akwai matsala gabanin zaɓukan shi ne ƙaruwar arangama tsakanin magoya bayan jam'iyyun siyasa daban-daban.

Kara karanta wannan

Yan Ta'adda Sun Kai Sabon Farmaki a Jihar Arewa, Sun Yi Awon Gaba Da Manoma Masu Yawa

Kwamishinan yaɗa labarai da ilimantar da masu jefa ƙuri'a na INEC ta ƙasa, Mista Sam Olumekun, shi ne ya nuna damuwar hukumar a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce a zaman da INEC ta yi da jam’iyyu, ta buƙaci su jajirce wajen ganin sun dakile magoya bayansu daga aikata ayyukan da za su iya kawo cikas ga gudanar da zabe cikin lumana a Nijeriya.

A ruwayar Vanguard, Sam Olumekun ya ce:

“INEC ta na ƙara kira da babbar murya ga dukkan jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da su guji kalamai na tunzura da ayyukan da ka iya zafafa harkokin siyasa."
"Hukumar zaɓe za ta ci gaba da sanya ido sosai kan lamarin da kuma tattauna wa da hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki domin ganin an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali a jihohin uku.”

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Babban Malami da Wani Mutumi Kan Muhimmin Abu 1 a Birnin Abuja

Halin da ake ciki kan shirye-shirye zaɓukan Imo, Bayelsa da Kogi

Dangane da batun wakilan jam'iyyu kuma, kwamishinan INEC na ƙasa ya ce tuni suka sanar da dukkan jam'iyyun siyasa cewa an buɗe shafin yanar gizo da zasu tura sunayen wakilan akwatunsu.

A cewarsa tun a ranar Alhamis, 24 ga watan Augusta aka bude shafin amma har kawo yanzu jam'iyyun ba su kammala tura sunayen ba a jihohin guda uku.

Zaben 2023: Sharri Aka Yi Mani, Ban Goyi Bayan Atiku a Boye ba Inji Jigon APC

A wani rahoton kuma Chukwudi Dimkpa ya wanke kan shi daga zargin da ake jifansa da shi na cin amana da kuma yin zagon-kasa ga jam'iyyar APC.

A wani jawabi da ya fitar a jiya, Chukwudi Dimkpa, ya ce bai cikin wadanda su ka yi taro da PDP , ya gargadi Okocha a kan raba kan APC.

Kara karanta wannan

Babbar Matsala 1 Da Aka Gano Bayan Taron da Atiku Ya Gudanar Kan Shugaba Tinubu a Abuja

Asali: Legit.ng

Online view pixel